Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Kimanin dalibai 400 ne wadanda suka kammala NCE a kwalejin ilimin jihar Yobe dake Gashuwa (Umar Suleiman College of Education, Gashu’a) suka sha rantsuwa da yin rijista da hukumar kwararrun malamai ta kasa ta Teachers’ Registration Council of Nigeria (TRCN), a karon farko da kwalejin ta gudanar da wannan shirin tun bayan kafuwar ta.
Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye, shi ne shugaban hukumar TRCN wanda Daraktan kwararru da tsare-tsare a hukumar ya wakilta, Malam Adamu A. Bello a wajen bukin yiwa daliban rijista da rantsuwar kasancewar su halastattu malamai tare da mika musu takardar shaidar hukumar kwararrun malamai ta TRCN.
Mr Ajiboye ya yaba wa shugaban kwalejin, Malam Muhammad Gishiwa da cewar ya yi amfani da kwarewar sa wajen dawo da martabar makarantar, tare da bayyana shi da gwarzo wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen bunkasa ilimi. Sannan ya ce “kuma ta dalilin irin wannan jajircewa da salon shugabanci nagari ya jawo TRCN ta zo don yiwa kwararrun malamai kuma wadanda suka sami horo nagari rijista a karo na farko. Me yasa can baya bamu zo ba- muna rijistar kwararru ne kawai”. Ya bayyana.
Shugaban hukumar ya kara da cewar, hukumar ta tsayu wajen bunkasa da kyautata ci gaban kwararrun malamai a farfajiyar cancanta, inda ya ce hakan zai baiwa malaman zarafin gano zurfin kwarewar sa tare da sanya shauki da karsashi a zukatan wadanda suka dauke su aikin koyarwa. Haka kuma ya gargadi sabbin malaman da cewa su kasance jekadu kuma malamai nagari su guji bin son zuciya da zai shafawa malanta bakin fenti da karya dokokin dake shimfide a dokar TRCN (Act Cap T3 of 2004), ya ce bi ta kan dokar na iya jawo kora da dauri ga mai laifin.
Da yake tofa nashi albarkacin baki, shugaban kwalejin Malam Muhammad Gishiwa ya yaba da namijin kokarin hukumar TRCN da” na yi imanin cewar ta dalilin rashin ingantaccen tsarin sanin ina aka dosa a tsarin malanta ya haifar da tunanin kirkiro wannan cibiya, domin dawo da martabar fannin, kuma bisa ga dukkan alamu tafiya ta mike wajen kaiwa ga kwalliya ta biya kudin sabulu”. Inji Malam Gishiwa.
“Cibiyoyin horas da malamai kamar irin tamu, suna aiki tukuru tare da ganin sun ba maras da kunya dangane da aiwatar da manufofin gwamnati a kan ilimi a karkashin hukumar kula da kwalejiji ta kasa(NCCE ), wajen samar da nagartattu kuma kwararrun malamai domin bayar da kulawa ta musamman a kananan makarantun mu”.
Malam Muhammad Gishiwa ya sake nanata cewar ”ko shakka babu, muddin wadannan kwararru kuma horarrun malamai zasu iya taka kowacce marhala a karkashin kulawar TRCN, kuma bisa hakikanin gaskiya, za a samu ci gaba mai ma’ana nan gaba a sha’anin malamanta a Nijeriya”. Ya nanata.