Biyo bayan zuba Naira tiriliyan 1.5 a Bankin Aikin Noma wanda gwamnatin tarayya ta yi a 2025, ana sa ran shekarar za ta kasance cike da gudanar da dimbin ayyukan aikin noma a kasar.
Wannan kuwa ya faru ne, sakamakon yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wannan kudi, musamman don a kara bunkasa aikin noma a Nijeriya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Rukunin Farko Na Taraktoci Dubu Biyu Daga Belarus
- Ba Gwamna Bala Ne Ya Soke Hawan Daushe Ba – Masarautar Bauchi Ta Bayyana Gaskiya
Babban Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya sanar da haka.
Ministan ya sanar da haka ne, lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga Bankin Bunkasa Aikin Noma daga Nahiyar Turai (EBRD) a Abuja, ranar Larabar da ta gabata.
Har ila yau, ya alakanta zuba wadannan makudan kudade a matsayin wani sabon sauyi da ba a taba samu ba a wannan fanni na aikin noma.
Kyari ya ci gaba da cewa, wannan bangare na noma don samun riba; shi ma zai amfana da Naira biliyan 500, wanda ya kai kimanin dala biliyan 300, wanda su ma wadannan kudaden za a bai wa Bankin Aikin na Noma.
Kazalika, Kyari ya yi kira ga Bankin EBRD, da ya zuba hannun jari a fannin aikin noman kasar, domin kasar ta cimma burin da ta sanya a gaba, musamman domin Nijeriya ta rage asarar da take yi a yayin girbin amfanin gona da samar da kayan aikin noman rani da sauran makamantansu.
Dakta Heike Harmgart, Manajan Daraknatan Bankin na EBRD da ke kula da yankin Afirka, wadda kuma ta jagoranci tawagar a nata jawabin ta ce, tawagar ta kawo ziyara ne ga Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci na kasar nan ne, sakamakon Nijeriya a kwanan baya ta zuba shaya ko hannun jari, domin gano bangarorin da ya kamata Bankin EBRD ya zuba hannun jarinsa a fannonin tattalin arzikin kasar.
Ta kara da cewa, Bankin na EBRD, zai yi aiki da Bankunan kasar nan; domin kara bunkasa zuba kudade a fannin aikin nomar kasar, inda ta ce; Bankin zai kuma bude ofishinsa a Jihar Legas.
“Muna kuma shirin daukar ‘yan Nijeriya masu hazaka, a bangarorin tattalin arzikin kasa, kuma a taron da za mu gudanar a watan Mayu na shekara-shekara, za mu gabatar da takardar bukata ga Nijeriya, kan bangarorin da za mu zuba hannun jari a kasar”, in ji Dakta Heike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp