Muhammad Maitela" />

Dalilin Da Ya Sa Ba Na Sallar Juma’a A Masallacin Kasa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, dalilinsa na yanke sharar yin sallar Juma’a a masallacin Juma’ar da ke Fadar shugaban kasa maimakon zuwa babban masallacin kasa da ke Abuja shi ne, domin kada ya jefa mutane cikin takura lokacin tawagarsa za ta wuce.
Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayar da wakilan limamai daga jihohin kasar nan da manyan malamai daga dukkanin jihohin kasar nan da birnin tarayya karkashin jagorancin Murshid na babban masallacin kasa da ke Abuja Farfesa Shehu Ahmad Galadanci.
“Dangane da bukatar da kuka nuna ta in dinga zuwa sallar Juma’a a masallacin kasa, ina so ku fahimce cewa, dalilina na yin sallar Juma’a a masallacin da ke Fadar shugaban kasa, shi ne, saboda kada sanadiyyar zuwa in takura al’umma daga ci gaba da walwala, musamman wadanda ke kan hanyar masallaci da kuma bayan an idar da sallah.
“ Kamar yadda duk kuka sani matukar shugaban kasa zai je wani wuri ana tsananta bincike a kan hanya, wanda kuma hakan zai haifar da cunkoson ababen hawa da na mutane,” Shugaban kasar ya gaya wa malaman hakan ne lokacin da suka kai masa ziyarar taya shi murnar samun nasarar sake zama shugaban kasa karo na biyu sakamakon lashe zaben da ya yi, wanda aka gudanar ranar 23, ga watan Fabarairu, 2019.
A karshe, ya gode wa malaman bisa gudummowar da suke ba gwamnatinsa ta hanyar yi mata kyawawan addu’o’i, musamman ta fuskar samun dawwamammen zaman lafiya a kasa baki daya.

Exit mobile version