Wake na daya daga cikin amfanin gonar da aka dakatar da shigar da da shi daga Nijeriya zuwa Tarayyar Turai.
Wasu kwararru sun yi gargadin cewa, akwai yiwuwar farashin Wake ba zai sauka ba a wannan kasa da muke ciki.
- Kakar Da Ta Fi Dacewa Da Noman Wake A Nijeriya
- Nazari Kan Lokacin Da Ya Fi Dacewa A Shuka Wake A Nijeriya
Kazalika, Cibiyar Kula da Fitar da Kayayyaki Kasashen Waje ta Kasa (NEPC) ta sanar da cewa, Nijeriya na noma Wake mai dimbin yawa; wanda ya kai kimanin kashi 58 cikin 100 na yawan wanda ake bukata a duniya.
Sai dai, wasu matsaloli da suka hada da ayyukan ‘yan bindigar daji, yawan rikice-rikice a tsakanin manoma da makiyaya da sauran makamantansu, an danganta su a matsayin manyan kalubalen da ke jawo rashin noman Waken da dama a Nijeriya.
Bugu da kari, akwai kuma kalubalen rashin kayan aiki; da suka hada da samar da wurin adana shi da rashin yin amfani da dabarun zamani, wanda hakan ya jawo rashin samar da wadatuwar sa a fadin wannan kasa.
Shugaban Kungiyar Manoma na Kasar, reshen Jihar Kano (AFAN); Alhaji Abdulrasheed Magaji Rimin Gado ya sanar da cewa, sauyin yanayi da kuma matsalar rashin tsaro, sun yi matukar taka muhimmiyar rawa wajen kawo raguwar noman wannan Wake.
An ruwaito cewa, Jamhuriyar Nijar; na tura kimanin kashi 45 cikin 100 na Waken da take nomawa zuwa wasu jihohin Arewacin Nijeriya, inda ake hada-hadar kasuwacninsa ta hanyar musayar Naira da kuma takardar kudin CFA, wanda hakan ko kadan baya taimakawa wannan fanni.
Magaji ya ci gaba da cewa, manyan dillalansa ba sa iya shigo da shi cikin wannan kasa, sakamakon matsalar samun kudaden musaya da ba sa iya samu.
Ya kara da cewa, lamuran na ci gaba da kara munana; musamman idan aka yi la’akari da wani rahoto da ya riske mu da ke nuna cewa, Jamhuriyar ta Nijar ta dakatar da fitar da amfanin gona daga kasar zuwa wasu kasashe, ciki har da Nijeriya.
A cewarsa, hakan ba zai bari farashinsa da sauran kayan amfanin gona su ragu ba.
Ya sanar da cewa, akwai matukatar bukatar a bai wa noman rani muhimmanci, musamman don cike gibin da aka samu a noman damina na bana.
Kazalika, ya sanar da cewa, ya zama wajibi gwamnati ta kayyade farashi, musamman a kan Wake domin samar da wadatuwarsa; cikin kuma farashi mai sauki.
Shi ma, wani babban dila a Kasuwar Hatsi ta kasa da kasa a Kasuwar Dawanau ta Jihar Kano, Alhaji Musa Gawuna ya bayyana cewa; ba a noman Wake da yawa, duk kuwa da matukar bukatar da ake da shi.
A cewarsa, wasu manoman; musamman na Waken, na kauracewa gonakinsu, saboda yawan samun rikice-rikicen manoma da makiyaya, wanda hakan ya dakatar da manoman daga yin nomansa kamar yadda aka yi tsammani.
Rahotannin sun ce, mahukuntan soji na kasar Nijar, sun dakatar da fitar da Shinkafa da sauran amfanin gona zuwa sauran kasashen duniya.
Sun dauki wannan matakin ne, biyo bayan barazanar da kungiyar ECOWAS ta yi wa mahukuntan kasar na cewa, tilas ne su mayar da kasar kan turbar mulkin dimokradiyya; bayan juyin mulkin da suka yi a kasar a shekarar da ta gabata.