Nijeriya za ta yi asarar samun wani sabon bashin a zango na biyu, kan kafa masana’antun noma na shiyya-shiyya (SAPZs).
Kasar za ta yi wannan asara ce, sakamakon jinkirin da aka samu na rashin wanzar da zango na daya na shirin, wanda yawan bashin ya kai kimanin dala miliyan 38.
Babban mai bai wa Shugaban Bankin Raya Nahiyar Afrika (AFDB), Dakta Akinwumi Adesina, Farfesa Oyebanji Oyelaran-Oyeyinka ne ya bayyana hakan.
- Rikicin Jam’iyyar NNPP Ya Kazanta A Kano
- Gwamnan Kano Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin 2025 Na Naira Biliyan 549.1
Farfesan, ya sanar da hakan ne a lokacin da ya gabatar da wata kasida ta shiri na musamman kan kafa masana’antun noma na shiyya-shiyya a wani taron bita na jihohin da suka amfana da kashin farko na shirin da aka gudanar a A.
Ya ce, ma’anar shirin; wata dabara ce ta zamani da za ta taimaka wa Nijeriya wajen fitar da ita daga matsalar rashin aikin yi da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Oyebanji ya kuma yi nuni da cewa, duba da jinkirin da ake fuskanta na wanzar da shirin kashi na daya tare da shirye-shiryen barin ofis na Dakta Akinwumi Adesina, a matsayin shugaban bankin; nan da shekaru biyu, hakan zai sa Nijeriya ta sake neman sake ciwo wani bashin daga bankin.
Har ila yau, ya kuma yi gargadin cewa; matukar Nijeriya ba ta tashi tsaye ba, zai yi wuya ta samu bashin a zango na biyu.
Haka zalika, sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa; ba a wanzar da wannan shiri ba, sakamakon guda daga cikin ministocin a wancan lokaci ya soki shirin a wani zama da majalisar zartarwa ta wancan lokacin ta yi.
Amma duk da haka, bayan Dakta Adesina ya zama shugaban bankin AFDB, ya wanzar da shirin; inda bankin ya rika taimaka wa kasashe da dama ciki har da Kasar Ethiopia, wanda ko shakka babu shirin ya samu dimbin nasarori.
A kashi na farko, shirin ya karade Jihohin Kuros Riba, Imo, Kaduna, Kano, Kwara, Ogun da Oyo da kuma Abuja, inda shirin ya bukaci zuba dala biliyan daya a fannin zuba hannun jari na masu zaman kansu, wanda hakan zai taimaka wa manoma wajen rage yin asara a girbin amfanin da suka samu na farko.
Kazalika, Oyelaran ya yi nuni da cewa; samun nasara a zango na daya na shirin ne, zai taimaka a amince da zango na biyu na shirin, wanda kuma ake da yakinin fadada shi a dukkanin daukacin fadin Nijeriya.
Har wa yau, shirin zai taimaka wa Nijeriya wajen samun damammakin amfana da fannin aikin noma da kuma kara bunkasa tattalin arzikinta.
Sai dai, Darakta Janar na bankin na AFDB a Nijeriya, Dakta Abdul Kamara, na da yakinin cewa; wata ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin suka yi a kwanakin baya a Abuja, an yi ta ne da nufin sake tattaunawa; domin gaggawar aiwatar da shirin.