Bisa wani rahoto da kungiyar kasashe masu samar da Man Fetur ta fiyar, ya bayyana cewa, kasar nan, ta ci gaba da rike Kanbyuna na na kasa mafi yawan samar da Danyen Mai a Afirka a watan Maris, da ya gabata.
Hakan na kunshe ne, a cikin wani sabon rahoton da kungiyar kasashe masu samar da Man Fetur,waro OPEC ta fitar.
- ‘Yan Sama Jannati 3 Na Kumbon Shenzhou-20 Na Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniyar Sin Cikin Nasara
- Masana’antun Nijeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 1.11 Wajen Samun Wutar Lantarki A 2024 – Rahoto
Kungiyar ta fitar da rahoton ne, na wata-wata a ranar Litinin, da ta gabata, wanda kuma ya nuna cewa, yawan Man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.40 a kowace rana.
A cewar kungiyar ta OPEC, wannan ya ya faru ne duk da raguwar yawan man da Nijeriya ta samar a watan da ya gabata, musamman idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairun da ya gabata.
Rahoton ya ci gaba da cewa, duk da raguwar, yawan Man da kasar nan ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce na kasashen Algeria da Dimoliradiyyar Kongo.
Kazalika, kungiyar ta bayyana cewa, ta hanyar ci gaba da karfin da ta samu a watan Fabrairu, kasar nan, dara kasar Algeria, inda ta samar da ganga 909,000 a kowace rana, da kuma jamuriyar Kongo da ta samar da ganga 263,000 a kowace rana.
Kungiyar ta kara da cewa, kasar nan, ta samar da ganga miliyan 1.51 a kowace rana a watan Maris da ya wuce, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.54 a kowace rana a watan Fabrairun da ya gabata.
Bugu da kari, hukumar kula da harkokin Man Fetur na kan tudu ta kasa NUPRC, ta bayyana cewa, yawan Man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga 1,400,783 a kowace rana a watan Maris da wuce.
Sai dai, a cewar hukumar, duk da raguwar yawan man da aka samar a watan Maris da ya gabata, matsakaicin yawan Danyen Man da aka samar a Nijeriya, ya kai kaso 93 cikin dari na adadin ganga miliyan 1.5 da kungiyar OPEC ta ware wa Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp