Shirye-shiryen Gwamna Uba Sani da ke da nufin inganta hada-hadar kuɗi da faɗaɗa hanyoyin biyan haraji sun kara habaka samar da kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) a jihar Kaduna sosai.
Shugaban Hukumar tattara kudin haraji ta jihar Kaduna (KADIRS), Mista Jerry Adams ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a karshen mako.
- An Zargi ‘Yar Siyasa Da Yunkurin Kashe Shugaban Kasar Malawi
- EFCC Ta Cafke Wadanda Suka Damfari Attajiri Aminu Dantata
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa, Jihar Kaduna ta kasance jiha ce da ta fi kowacce jiha a yankin Arewaci samun kudaden shiga a shekarar 2023, inda ta tara IGR, Naira biliyan 62.49
Wannan adadi ya sanya Kaduna a sahun gaba wajen samar da kudaden shiga a arewacin Nijeriya.
Mista Adams ya alakanta wannan nasarar da yadda ake sarrafa kudaden haraji a karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta hanyar aiwatar da tsarin “Pay Kaduna Portal,” wacce ta ba masu biyan haraji damar biyan haraji ta hanyar yanar gizo, ba tare da cewa, dole sai an ziyarci ofisoshin harajin ba.
Ya yi nuni da cewa, wannan tsarin na yanar gizo ya yi tasiri sosai wajen rage barnatar da dukiyar al’umma, wanda hakan ya sa masu biyan haraji suka samu sauki wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.