Connect with us

MANYAN LABARAI

Dalilin Komawata APC, Cewar Dogara

Published

on

  • Ba Zan Zauna A Jam’iyyar Da Rashawa Ta Yi Katutu Ba
  • Rashin Cika Alkawarin Gwamna Bala Ya Bazama Ni

A cikin makon da ya gabata ne tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya fice daga jam’iyyar PDP gami da tsunduma cikin jam’iyyar APC, lamarin da ya zama abin mamaki da ciza yatsa ga PDP, wacce ta misalta batun a matsayin “marar dadi sam!”

Da ya ke bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar, wanda ya aike da wasikar murabus ga shugaban PDP a gundumar ‘C’ da ke karamar hukumar Bogoro mai kwanan wata 24 ga Yuli, 2020, Hon. Dogara ya shaida cewar, rashin alkiblar da gaza cika alkawuran gwamnati mai ci a Jihar Bauchi na daga cikin dalilansa na barin jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewar, da kimarsa da mutuncinsa tun da ya hango gwamnati mai ci ta PDP a jihar ta sauka daga layin cika alkawuran da su ka yi wa jama’a a lokacin yakin neman zaben 2019 tare da sauya alakarta zuwa ga wata manufa na daban ya ga dacewar barin jam’iyyar, domin kare kimarsa da mutuncinsa.

Ya ce, ko a zaben 2019 sun hada kai da PDP ne da zummar kawo sauyi mai ma’ana ga jihar ta Bauchi ne, sai kuma ya misalta lamarin da cewa abinda ya tsammata sam ba haka ya riska ba.

“Na rubata ne, don na sanar da daukar matsayar ficewata daga jam’iyyar PDP. Hakan ya zama dole a gare ni ne a sakamakon cewa, ni na hada kai da ku a zaben 2019, domin tabbatar da canji mai ma’ana a jiharmu ta Bauchi.”

Kai tsaye dai Dogara ya gabatar da wasu tambayoyi da su ke nuni da zargin gwamnati mai ci a jihar da babakere.

Dogara ya yi tambayar cewa, ya a ka yi da kason kananan hukumomin jihar tun daga watan Mayun 2019 tare da ina alkawarin gudanar da zaben kananan hukumomi cikin wata shida da jam’iyyar PDP da alkawarta a lokacin da su ke neman jama’a su zabe su?

Ya ce, “Ina Naira biliyan N4.6 na bashin da a ka karba a banki da biya su kai tsaye ta asusun ajiyar wani kamfani mai zaman kansa. Ina kudin su ka buya?”

Ya kuma yi tambaya kan cewar me ya sa biyan albashin ma’aikatan jihar ta Bauchi ke da alaka da wani kamfani mai zaman kansa a matsayin masu bada shawara?

Tsohon Kakakin ya kuma gabatar da wata tambaya da ta ke da alaka da hanya da gwamnatin Bauchi ke bayar da kwangiloli ta hanyoyin da su ka kauce wa ka’idar bayar da su.

“Saboda haka, ta wannan wasikar na fice daga jam’iyyar PDP,” Inji Hon. Dogara.

Shi dai Yakubu Dogara ya na daga cikin muhimman mutanen da su ka taimaka wajen kawo gwamnatin Sanata Bala Muhammad a Jihar Bauchi, wadanda su ka hada kai tare da yakar Barista Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin Gwamnan Jihar tare da mara wa Sanata Bala baya, inda kuma tun ba a kai rabin wa’adin Mulkin ba ya nuna rashin gamsuwarsa da salon Gwamna Bala.

Kawo zuwa aikawa da rahoton nan daren jiya, Wakilin LEADERSHIP A YAU ya yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Gwamnan Bauchi, Muktar Gidado, amma abin ya ci tura, inda ya riske wayarsa a kashe.
Advertisement

labarai