Dalilin Maye Gurbin Lambar BVN Da Ta Dan Kasa – Pantami

Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke shirin maye gurbin lambar BVN da lambar zama dan kasa.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen gudanar da kafin dan kasa dake Babban Birnin Kasar, Abuja, inda ya kara da cewa, zai gana da kwamitin farfado da tattalin arziki da gwamnan babban bankin Nijeriya domin mika bukatar hade BVN da lambar katin zama dan kasa. A cewarsa, lambar BVN manufarta shine ita ce, samun kulawa da sa ido, yayin da lambar katin zama dan kasa doka ce.

Ya ce, “karfin doka ba za a taba hada shi da manufofi na wata cibiya guda daya ba.”

Ministan ya kara da cewa, lambar BVN yana takaita ne ga wadanda suke da asusun banki, yayin da lambar dan kasa doka ce ga duk wanda yake zaune a Nijeriya.

“Lambar BVN shi ne kididdigan bayananmu na biyu, yayin da lambar katin zama dan kasa shi ne ke da matsayi na farko a kan kowani dan kasa da kuma kowata ci bya da ke cikin Nijeriya,” inji shi.

Pantami ya yi alfari da Nijeriya a matsayin uwa da yankin Afirka wacce ya kamata ta kare kulawa da bayanai da kuma daukan matakai sabra da tsaro wanda za a iya samu a cikin bayanan kididdiga wanda zai kai kashi 99.9.

Ya ce, “sakamakon wannan dadilin ne ya sa Nijeriya ta tilasta bin hanyoyin da ba a samu kididdige mutane cikin sauki wanda ta haka ne za a samu dakile wasu daga cikin hanyoyin rashin tsaro.

“Za mu tabbatar da cewa, an samu cikakken tsaro a cikin kasar nan, sannan ba za mu taba amince ba wani ya ballo da wani shiri na daban, domin ‘yan kasa sun amince da mu.”

Da yake bayar da dalilan da gwamnatin tarayya ta bukaci kamfanoni masu zaman kansu su gudanar da katin zama dan kasa, ministan ya bayyana cewa, yin hakan yana daga cikin tsarin kasashen duniya. Ya jaddada cewa, akwai bukatar hukumar kula da katin zama dan kasa su gudanar da aiki tukuru wajen yin rijsta yadda ya kamata kamar wajen kayyade tsawan mutane da sauran cikkun bayanai na ‘yan kasa. Pantami ya bayyana cewa, wannan tsari ba karamin ci gaba ba ne, inda ya bukaci kamfanoni masu zaman kansu da su kada kai da gwamnati wajen gudanar da aikin yadda ya dace. Ya ce, a halin yanzu tattalin arzikin Nijeriya ya dogara ne da yadda zamani ke tafiya.

Pantami ya ce, wannan hanya da hukumar samar da ayyuka ta kasa da kuma shirin gwamnatin tarayya na musamma na gudanar da ayyuka guda 11,000 wanda zai ciro matasa wadanda ba su da aikin yi a Jihar Gombe tare da ba su ayyukan da za su dogara da kansu. Ya ci gaba da cewa, samar da mahallin da ya dace wajen kafa kamfanoni masu zaman kansu, shi ne zai sa a sami harkokin kasuwanci da ya dace.

Minista ya ce, “a halin yanzu tattalin arzikin Nijeriya ya dogara ne da kamfanoni masu zaman kansu fiye da bangaren gwamnati.

“Idan muka kalli kudaden shigan da gwamnati take samu a halin yanzu, za mu ga mai wuce dala biliyan 450 wanda shi ne mafi kololuwa duka a yankin Afirka. Idan aka kwatanta da gaba daya ayyukan da gwamnatin tarayya take gudanarwa, wannan kai kashi 8.5, yayin da kamfanoni masu zaman kansu suke da kashi 91.5. gwamnatin tarayya ba za ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba sai dai ta hada kai da kamfanoni masu zaman kansu.

“Abin da gwamnatin tarayya za ta yi a yanzu shi ne, samar da katin zama dan kasa tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, wannan shi za mu yi wajen fitar da wasu tsare-tsare da za su tallafa wa kamfanoni masu zaman kansu domin gudanar da aiki yadda aka tsara.

“Wannan ne ya kai ga saka haraji a cikin hutu da bayar da izini ga wannan zai shigo Nijeriya da kuma gudanar da yin rijistar kamfanoni a yanar gizo ga hukumar da ke kula da kamfanoni a Nijeriya,” in ji minista.

Ministan ya yaba wa ma’aikatan da ke aikin yin katin dan kasa bisa gudanar da aiki ba dare babu rana domin samun ayyuka mai inganci.

Exit mobile version