• English
  • Business News
Thursday, August 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
5 days ago
in Rahotonni
0
Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yayin da a ke kasa da shekaru biyu gabanin gudanar da babban zaben 2027, jam’iyyun siyasa na ci- gaba da fuskantar matsaloli nan da can a kokarin ganin sun samu rinjaye.

Masu fashin bakin lamurran siyasa na ganin yadda ‘yan siyasa suka jawo zaben kusa wajen fara shirye-shirye da wuri zai yi zafin da zai dama ya shanye zaben da ya gabata ta bangarori da dama.

  • Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
  • Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

Yadda jam’iyyar APC da ke kan gadon mulki ke shige da fice wajen jawo jigogin jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar domin kara mata karfi tare da kokarin kare lagon jam’iyyun adawa ya nuna a fili irin fargaba da zullumin da jam’iyyar mai mulki ke yi na shan kaye.

Haka ma yadda talakawa da sauran al’umma suka kagara lokacin zaben ya gabato domin su yi amfani da kuri’un su wajen zaben shugabannin da suke muradi ya nuna a fili zaben zai dauki hankalin al’ummar ciki da wajen kasa.

A tarihin siyasar Nijeriya al’ummar kasa ba su taba fuskantar halin matsi, kuncin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki irin na wannan lokacin a karkashin jagorancin jam’iyyar APC ba wanda hakan zai iya tasiri a akwatin zabe.

Labarai Masu Nasaba

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

A yanzu haka manyan jam’iyyun siyasa na fuskantar kalubale musamman rikicin cikin gidan kan shugabancin jam’iyyun wanda hakan matsala ce da idan ba a samu maslaha ba wani bangaren kan iya canza sheka ko zagon kasa ga jam’iyyar wanda zai iya shafuwar makomarta a 2027.

Ya zuwa yanzu jam’iyyun APC da sabuwar jam’iyyar hadaka ta ADC suna yakar juna kan wace jam’iyya ce ke da goyon bayan yankin Arewa, yankin da shine ke tabbatar da nasarar kowane dan takarar shugabancin kasa a Nijeriya.

A yayin da jam’iyyar APC wadda shugaba Tinubu ke kan wa’adin mulki na farko tare da yunkurin neman sake zabensa a karo na biyu; jam’iyyun adawa ciki har da PDP wadda APC ta karbe mulkin kasa a hannun ta, ta hanyar kayar da ita zaben 2015, na yin duk mai yiyuwa domin ganin mulki ya dawo a hannun su.

Bankwana da Atiku Abubakar ya yi daga jam’iyyar PDP ya bube kofar jam’iyyar ga neman wanda zai tsaya mata takara a zabe mai zuwa musamman domin cike gibin da tsohon mataimakin na Shugaba Obasanjo ya bari.

 

Dawowar Jonathan

A kan wannan, a yanzu haka rahotanni sun nuna cewar tuni jam’iyyar PDP ta bukaci tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan da ya aminta ya tsayawa jam’iyyar takara a zabe mai zuwa.

Idan har Jonathan ya aminta da tsayawa takara a jam’iyyar PDP kuma ya samu nasara, to zai gudanar da wa’adin mulki daya ne kawai zuwa 2031 kasancewar ya riga ya gudanar da wa’adi na farko tare da shan kasa a neman wa’adi na biyu a hannun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Wata majiya da ba a tabbatar da sahihancin ta ba, ta kusa da tsohon shugaban ta bayyana cewar Jonathan ya aminta da tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Majiyar ta bayyana cewar tuni kokarin tsayar da Jonathan takara ya yi nisa domin har ya aminta da tayin da aka yi masa daga jam’iyyarsa wadda ya gudanar da shugabanci a karkashin ta.

A cewarsa tsohon shugaban ya karbi bukatar tsayawa takara ne domin samun damar magance matsalolin talauci da kuncin da al’umma ke fuskanta tun bayan da jam’iyyar APC ta karbi mulki a 2015.

Majiyar ta ce tuni Jonathan ya hadu da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa a ciki da wajen PDP musamman daga yankin Arewa domin tuntubar su da neman goyon bayan su.

Kamar yadda dan siyasar ya bayyana Jonathan ya hadu da tsohon shugaba, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a kwanan nan a gidan da da ke Minna ya kuma fada masa niyarsa ta tsayawa takara a 2027.

Haka ma mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Malam Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da cewar lallai PDP ta fara yunkurin dawo da Jonathan.

Ya ce ‘yan Nijeriya da dama sun fahimci kuskuren da suka yi na kin sake zaben Jonathan. A yanzu sun gano irin kokarin da ya yi da nasarorin da aka samu a mulkinsa tare da neman afuwa da rokon sa kan ya dawo ya ceto kasar nan.

A nasa ra’ayin tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido na ganin tsohon shugaban kasa Jonathan na da aikin da bai kammala ba a fadar mulki don haka shine mafi cancantar zama dan takarar PDP da zai kalubalanci Tinubu.

Idan har ta tabbata Jonathan zai tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP to ya zama babban kalubale ga jam’iyyar hadaka ta ADC wadda ke fafatukar hada kan jigogin PDP da na wasu jam’iyyu zuwa jam’iyyar domin tunkarar APC gaba da gaba a zaben 2027.

‘Yadda ‘yan siyasa kama daga Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Ameachi da tsohon shugaba Jonathan ke kokarin ganin sun samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyun ADC da PDP ya zafafa farfajiyar siyasar kasar nan.

Tsayawa takarar a cikin lokaci, ba wai lamari ne kawai na wane ne zai fuskanci shugaba Tinubu a zabe ba, haka ma wane ne zai samu nasara a zaben. Bugu da kari lamari ne na rike jam’iyya, tabbatar da siyasar hadaka da tsare-tsaren da za su magance matsalolin gabar siyasa da shawo kan matsalar sabbin ‘yan takara.

 

Atiku Abubakar

Fitar tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar daga PDP wanda shine babban jagoran jam’iyyar ya haifar da canza shekar dimbin jama’a daga jam’iyyar wadda ta jima rike da kambun babbar jam’iyyar adawa a kasar nan.

Duk da cewar ya zuwa yanzu Atiku Abubakar bai shiga jam’iyyar ADC a hukumance ba, amma tabbataccen abu ne yadda yake da ruwa da tsaki a jam’iyyar.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, wasu mukamai a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da kwamitin amintattu da shugabannin jihohi duk mutanen Atiku ne suka mamaye a ADC. Wannan matakin kamar yadd masu sharhin al’amurran siyasa suka bayyana mataki ne na ganin Atiku ya samu tikitin jam’iyyar.

A yanzu hakta a tsohon mataimakin Shugaban Kasa, bai ce komai ba kan kudurinsa ba, amma alamomi sun tabbatar da cewar zai tsaya takarar shugabancin kasa domin fafatawa da shugaba Tinubu.

 

Kalubale A Hadakar Obi

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya shiga cikin hadakar jam’iyyar ADC da tsammani mafi girma.

Tsohon Gwamnan Anambra na ganin dan takara ne da ke da cancanta da gogewar siyasa wanda ke da kwarewar da zai iya canza makomar kasar nan a cikin shekaru hudu, kamar yadda ya bayyana cewar ba zai wuce wa’adi daya ba.

Shigar Obi a ADC ba tafiya ce mai sauki ba, domin kuwa a watan Agusta da muke ciki wata takarda ta bayyana daga magoya bayyansa da ke korafin ware su a muhimman mukaman zartaswa a jam’iyyar.

Magoyan bayan sun nuna damuwa kan yadda shugabannin jam’iyyar suka mayar da su saniyar ware a lamurran jam’iyyar wadanda ake da tabbacin sun yi hakan ne domin goyon bayan da suke yi wa Atiku Abubakar.

A cewarsu a ba a gayyatarsu a mafi yawan tarukan jam’iyyar da ake daukar muhimman matakai kan hadakar wanda hakan ya nuna bangaranci da kin tsayuwa kan gaskiya wanda muhimmin abu ne a dorewar kawance.

A yayin da yake ci-gaba da samun karbuwa a duniyar gizo, babu tabbacin Obi zai samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyar ADC, a bisa ga yadda Atiku Abubakar ya mamaye jam’iyyar da jagororin ta.

 

Kokarin PDP Na Jawo Obi

A yayin da Obi ke ci- gaba da fuskantar matsalar siyasar cikin gida ta hadaka, PDP ba za ta zauna ba tare da daukar mataki ba, domin kuwa shugabannin jam’iyyar da dama ciki har da shugaban kungiyar Gwamnonin PDP, Bala Muhammad sun bukaci ya dawo jam’iyyar.

PDP na ganin dawowar Obi ba wai kawai za ta karfafawa jam’iyyar ba ne kawai wajen lashe zabe ba haka ma mataki ne na sake hadewa da jigogin jam’iyyar da aka raba gari.

Sai dai ba dukkanin magoya bayan jam’iyyar PDP ne ke ganin cancantar Obi ta tsayawa takara a 2027. Wasu da yawa na ganin alkawalinsa na gudanar da wa’adin zangon mulki daya tatsuniya ce kawai.

A tattanawar sa da manema labarai a kwanan nan, wani jigon PDP, Umar Sani ya bayyana cewar Arewa za ta fi bukatar Jonathan ya zama dan takara a kan Obi domin a cewarsa kalamansa na gudanar da shekaru hudu kacal, zance ne kawai na siyasa.

 

Karon Battar PDP Da ADC

Jam’iyyun PDP da ADC na ci-gaba da nunawa juna yatsa wadanda duka suna ci-gaba da rike magoya baya daya wadanda kuma ke bukatar karin goyon bayan jam’iyyun adawa musamman wadanda ke ganin APC ta gaza.

Idan har jam’iyyar PDP ta samu nasarar dawo da Obi a cikin ta, za ta raunana matsayin jam’iyyar ADC da wargaza hadakar da ta assasa. A daya bangaren idan kuma ADC ta tsayar da Atiku ko Obi za ta kalubalanci mamayar da PDP ta yi a matsayin babbar jam’iyyar adawa.

Za a gudanar da karon batta mai karfi domin dukkanin jam’iyyun sun gamsu da cewar duk wanda ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar a zaben share fage yana da cikakkiyar damar karbar mulki a hannunn APC a 2027.

Duk dai yadda kaya, a watanni masu zuwa za a ga shin ko wadannan ‘yan takarar za su yi gaba da gaba ko fito na fito da juna ko samun hanyar kawance domin samun kakkarfar hadaka da za ta gwabza tare da yin awon gaba da APC ko akasin hakan

A bayyane yake dai fafatawar ADC da PDP a neman tikitin takarar shugaban kasa ya wuce yakin neman amincewar jam’iyya, domin fafatawa ce da za ta iya canza makomar siyasar kasar nan a 2027.

 

APC Ta Sha Jinin Jikin Ta

Yadda jigogin siyasar kasar nan suka daura damarar tunkarar babban zaben 2027 da dukkan karfin su ya sanya APC da ke kan mulki shan jinin jikin ta a bisa ga kuka da kokawa da jama’a ke yi da salon mulkin ta.

Babbar matsalar da jam’iyyar APC ke fuskanta a yanzu haka shine yadda dimbin jama’a suka dawowa da rakiyar jam’iyyar wadda suka ce ta na gudanar da salon mulki mai taken “sai kow kowa ya jiya a jikinsa.”

Masu fashin bakin lamurran siyasa da dama na ganin yadda kasar take a rikice bisa ga tabarbarewar lamurran tsaro, da tsadar rayuwar da jama’a ke fuskanta ba abin da zai sa jama’a su sake zaben jam’iyyar.

Al’ummar kasa wadanda ke shan ukuba a bisa ga cire tallafin man fetur na kukan inda gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi ke kai makuddan kudaden da suke samu wadanda suka zarce na gwamnatocin baya, domin ba su ga canji a kasa ba.

Shugaba Tinubu wanda ke sane da kuncin da jama’ar kasa suka kara shiga bayan karbar mulkinsa bai dauki kwararan matakan magance dimbin matsalolin da suka yi wa jama’a katutu ba wanda hakan ya baiwa jam’iyyun adawa damar yekuwar neman zabe a cikin sauki.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Siyasa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima

Next Post

APC Ta Nemi A Soke Zaɓen Cike Gurbi A Kano Saboda Rikici

Related

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya
Rahotonni

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

5 days ago
Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda
Rahotonni

Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

6 days ago
Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Rahotonni

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

4 weeks ago
Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
Rahotonni

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

4 weeks ago
Fyade
Rahotonni

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

1 month ago
APC
Manyan Labarai

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

1 month ago
Next Post
APC Ta Nemi A Soke Zaɓen Cike Gurbi A Kano Saboda Rikici

APC Ta Nemi A Soke Zaɓen Cike Gurbi A Kano Saboda Rikici

LABARAI MASU NASABA

Boniface

Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface

August 20, 2025
Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe

Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe

August 20, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

August 20, 2025
Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa

Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa

August 20, 2025
Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabbin Makamai Yayin Faretin Soja Na Ranar 3 Ga Watan Satumba

Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabbin Makamai Yayin Faretin Soja Na Ranar 3 Ga Watan Satumba

August 20, 2025
Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a 

Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a 

August 20, 2025
Xizang A Shekaru 60 Da Kafuwa: Daga Mawuyacin Hali Zuwa Farin Wata Sha Kallo

Xizang A Shekaru 60 Da Kafuwa: Daga Mawuyacin Hali Zuwa Farin Wata Sha Kallo

August 20, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Watsi Ga Ƙarin Girma Ga ASP 179, Ta Ɗaga Darajar 952 Zuwa DSP

August 20, 2025
Xi: Wajibi Ne A Aiwatar Da Dabarun JKS Wajen Mulkin Yankin Xizang Na Sin A Sabon Zamani

Xi: Wajibi Ne A Aiwatar Da Dabarun JKS Wajen Mulkin Yankin Xizang Na Sin A Sabon Zamani

August 20, 2025
Xi Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 60 Da Kafuwar Yankin Xizang

Xi Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 60 Da Kafuwar Yankin Xizang

August 20, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.