Wani abu ne sananne kuma na al’ada, a samu wasu rigingimu nan da can, bayan kammala gabatar da zabukan cikin gida na jam’iyya, kuma irin wannan dambarwa na samuwa ne cikin kowace irin jam’iyya, musamman wadda ke da karfin magoya baya.
Dalilan da ke haddasa irin wadancan rigingimu da aka ambata a sama na da tarin yawa, sannan a wasu lokuta suka canja salo daga wannan lokaci zuwa wancan, koko daga wannan nahiya zuwa waccan. Bugu da kari, yayin afkuwar irin wadancan rikice-rikicen, wasu kan samu sulhuntuwa ne tun daga matakin jam’iyya, ta yadda za a lallashi wasu ko wani daga cikin “yan takarar, a nemi da ya koma neman wata kujerar. Misali, mai neman kujerar majalisar dattijai, sai a tura shi neman kujerar majalisar wakilai.
A dai cikin irin waccan dambarwar takarar kujerun mukaman iko na gwamnati, a kan lallashi mai neman kujerar gwamna ya koma neman ta Sanata, kamar yadda a jihar ta Kano aka lallashi Sanata Barau Jibril, na ya hakura da takararsa ta kujerar gwamnan Kano karkashin jam’iyyar APC, ya koma neman kujerar Sanatan Kano ta Arewa.
Bugu da kari, a wasu lokuta ma, ba ta kai wa ga fara samun dambarwa, sai a ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyya sun yanke hukuncin yadda “ya”yan jam’iyya za su nemi kujerun na takara.
Misali, a Kano, Kwankwaso ya nemi Aliyu Sani Madaki, da ya hakura da neman kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, ya bar wa Sanata Malam Ibrahim Shekarau, a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP.
A wasu lokuta, irin wadancan rigingimu kan gagari kundila wajen warware su, ma’ana, su kan fi karfin sulhuntuwa a matakin jam’iyya.
Misali, danbarwar kujerar Sanata a jihar Yobe a yau, tsakanin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, da kuma wanda jam’iyya ta turawa hukumar INEC ta kasa sunansa : wanda daga baya, masu jam’iyyar su ka nemi da ya bar wa Ahmad Lawan kujerar, amma ya yi kememe.
A nan Kano, daga cikin “yan takarar kujerar gwamna a mabanbantan lokuta, wadanda rikice-rikicen da suke haduwa da su kan gagari sulhuntuwa a matakin jam’iyya, akwai dantakara Muhammad Sani Abacha. Wanda tun daga lokacin da ya fara sako kafarsa cikin harkokin siyasa a Kano da sunan wata takara, za a ga cewa, kujerar gwamna yake ta kokarin ganin ya samu, tare da yin aiki tukuru, don ganin mafarkin nasa ya tabbata.
Cikin Shekarar 2011
Muhammad Abacha ya nemi takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar CPCn Baba Buhari, amma irin kwamacalar da aka rika samu cikin jam’iyyar, da sunan takarar shugabancin jam’iyya ko na kujerun mulki, za a ga cewa ko kare ma ba shi ci. Muhammad Sani Abacha, Gen. Lawan Jafaru Isa (rtd), Dr Auwalu Anwar, Sanata Rufa’i Sani Hanga da marigayi Engr.
Magaji Abdullahi, sune jiga-jigan mutane sanannu daga cikin wadanda ke neman kujerar gwamna a wancan lokaci. Na’am, ba ya ga su, akwai ma wasu da ke neman kujerar ta gwamnan.
A karshen fim din CPC cikin Shekarar 2011, ta tabbata cewa dan Abachan ne ya samu nasarar lashe za6en kujerar gwamna, amma a karshen lamari, sai uwar jam’iyya ta kasa, ta hau kujerar-naki, ta bai wa Lawan Jafaru Isa takarar, duk da cewa Mohammed Abacha ne halastaccen dan takara da hanyar kada kuri’a.
Takarar Muhammad Abacha Da Jagororin Jam’iyya, 2011–2022
Babu shakka a fili yake cewa, a duk lokacin da Muhammad Abacha ya fito takarar kujerar gwamna a jihar Kano, kan hadu da kalubale gami da tarnaki daga manya kuma hamshakan jagororin jam’iyya, bayan samun nasarar lashe za6e bisa gwadaben doka. Dadin dadawa, irin wadancan manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, sun kasance aminai ne ga mahaifinsa a lokacin da yake raye, wato marigayi Gen. Sani Abacha (rtd).
Duk da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Sani Abacha da shugaba Buhari, hakan bai hana su Buhari da sauran “yan kwamitin amintattu na jam’iyyar CPC daukar Lawan Jafaru Isa a matsayin dantakara, duk da ya fadi za6en, tare da yin fatali da Muhammad Abacha, duk da cewa shi ne ya samu nasarar lashe za6en na cikin gida na jam’iyya karkashin jam’iyyar a Shekarar 2011.
An yi ta yamutsa hazo tsakanin “yan jam’iyya da ke nuna goyon bayansu ga Muhammad Sani Abacha a wancan lokaci, da kuma jagororin jam’iyyar na Kasa. Cikin na jikin Muhammad Abacha a wancan lokaci kuwa akwai SSG na Kano na yanzu, wato Alhaji Usman Alhaji, Hon. Ibrahim Dan’azumi Gwarzo da sauransu.
A karshe dai, an kare ne a Kotu, inda Kotu ta tabbatarwa da Abachan takararsa. Sai dai masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ba su rungumi wancan hukunci na Kotu da hannu bibbiyu ba. Wannan dalili, shi ne babban abinda ya jaza faduwar jam’iyyar CPC wanwar a Kano.
Takarar Muhammad Sani Abacha, PDP–2022
Hatta cikin wannan Shekara ta 2022 da Muhammad Sani Abacha ya fito takarar kujerar gwamna a Kano, ya sake tafka karo da irin wadancan masu ruwa da tsaki na jam’iyya. Sanin kowane cewa, Ambasada Alh. Aminu wali, na daga manya kuma mashahuran mutane a cikin wannan Kasa, da su ka tsuguna su ka haife jam’iyyar PDP cikin Shekarar 1998. Sai a ka wayigari, Muhammad Sani Abacha, ya nuna bukatarsa ta neman kujerar gwamna karkashin wannan jam’iyya ta PDP a Kano, a wannan Shekara ta 2022. Tun daga lokacin da Abachan ya nuna begensa da waccan kujera ne, sai ya fara haduwa da wasu irin jerin tsarmakatai daga 6angaren jagora Aminu wali. Ko mai karatu ya san dalili? Dalilin bai wuce saboda dan Walin, wato Sadik Aminu wali, shi ma yana neman kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar ta PDP.
Za mu ci gaba a makon gobe cikin yardar Allah