Manoma a jihohi daban-daban a kaar nan, na cikin fargabar aukuwar ambaliyar ruwan da za ta iya kwarara zuwa cikin gonakinsu.
Wasu daga cikin jihohin sun hada da Kebbi da Bauchi da Zamfara da Sakkwato da Kwara da Ribas da Kuros Riba da sauransu.
Tuni dai, hukumar kula da yanayin ruwa ta kasa ta sanar da cewa, ruwan da ya taru a Kogin Neja zai iya zama babbar barazana ga gonakan manoma, musamman wadanda ke jihohin Kebbi da Neja da Kwara da Nasarawa da Kogi da Anambra da Delta da Edo da Ribas da kuma Bayelsa wadanda kogin ya ke ta su.
Bugu da kari, Darakta-Janar na hukumar kula da yanayin ruwa ta kasa, Mista Clement Onyeaso Nze a wani rahoton ta ya fitar, ya yi hasashen cewar za a fara samun ambaliya a kasar nan daga 6 ga watan Satumba a Jihar Kebbi.
Alalmisali, a daminar bara ambaliya ta jawo wa dubban manoma wadanda akasarinsu manoman shinkafa da masara ne a jihohin Kebbi da Bauchi da Zamfara da Sakkwato, da Kwara da Ribas da Kuros Riba da sauransu, babbar asara.
Masana a fannin aikin noma a kasar nan, sun bayyana cewa, ambaliyar za ta jawo karancin abinci a a kasar nan, inda hakan zai kuma haifar da hauhawar farashin kayan abinci.
Har ila yau, sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a daminar bara, ta jawo tashin farashin kayan abinci, misali, sai da farashin buhun masara a jihar Kano ya kai naira 20,000.
Bugu da kari, a jihar Binuwai kuwa, farashin ya kai naira 22,000; a birnin tarayar Abuja kuwa ya kai naira 24,000, inda a jihar Legas ta kai naira 25,000.
Lamarin na tashin farashin sakamokon aukuwar ta ambaliyar ruwa, sai da ya shafi farashin shinkafar da ake noma wa kasar nan, inda buhunta ya kai naira 55,000 a Abuja ya kai naira 58,000.
Wani masani a fanin samar da abinci ya sanar da cewa, kasar nan za ta iya aukawa a cikin matsalar karancin abinci.
Bugu da kari, a shekarar da ta gabata Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kebbi ta sanar da cewa, sakamakon ambaliar da ta auku a bara, ta lalata kimain kadada 450,000 na gonakin shinkafa tare da lalata kadada 50,000.
Bisa hasashen da aka yi, manoma a jihar ta Kebbi sun tabka asarar da ta kai ta sama da naira biliyan biyar.
Wani manomin shinkafa a jihar ta Kebbi Garba Bala ya bayyana cewa, sakamakon ambaiyar ta bara ya yi asarar kimain kadada 16,000.
Ya kara da cewa, ya samo rancen ne daga banki don ya kara habaka nomansa na shinkafar wasu kuma daga cikin manoman shinkafar da iftila’in na ambaliyar ruwan ta aukawa gonakan su da suka shuka shinkafar sun bayyana cewa, samo rance ne a karkashin shirin aikin ma na gwamnatin tarayya na Anchor Borrowers da ke karkashin kulawar babban bankin Nijeriya.
Shi ma wani manomin shinkafa a jihar Sani Muhammad ya ce, ambaliayar ta lalata masa kadada shida tare da wasu kadada da ya shuka masara.
An ruwaito Shugaba kungiyar manoma ta kasa Ibrahim Kabiru ya ce ambaliyar ta fi shafar gonakin shinkafa da dawa da sauran amfanin gona.
Kabiru ya kara da cewa, zai yi wuya a iya iyakance barnar da ambaliya ta haifar a gonakan manoman, inda ya bayyana cewa, a gefe guda kuma manoma a kasar, musamman a arewacin kasar nan na ci gaba da fuskantar barazanar rashin tsaro saboda hare-haren ‘yan bindiga, inda hakan ya tilasta wa maona da dama, kaurace wa gonakinsu don gudun kar masu garkuwa su sace su ko kuma su hallaka su a yayin da suka je gonakarsu don yin noma.