A yayin da daminar bana ta kankama sosai, wasu manoma da ke kasar nan, musamman a Arewacin kasar sun fara fargabar bullar tsuntsaye masu jan-baki wadanda ke lalata amfanin gonakinsu.
Bugu da kari, fargabar ta manoman ta zo ne lokacin da a kasar nan ake ci gaba da fuskanatar karancin abinci, musamman ganin yadda ‘yan bindiga suka hana yawancin manoman da ke fadin kasar nan, musamman na karkara zuwa gonakinsu domin nomansu.
A bara, wasu daga cikin kauyukana da wannnan annobar ta tsintsayen ta auka wa sun hada da, Tudun-Mai-Tandu da ke cikin karamar hukumar Dange Shuni a jihar Sakkwato, inda rahotanni suka tabbatar da cewa, irin wadannan tsintsayen sun yi wa gonakin manoman da ke kauyen kawanya, suka kuma lalata musu amfanin gonakinsu.
Ko a bara Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Sakkwato, Alhaji Sambo Abubakar ya bayyana cewa, tsuntsaye sun shiga gonakisnu, inda suka lalala musu Shinkafar da suka shuka.
A cewarsa,sakamakon shigar da tsuntsayen suka yi cikin gonakinsu, sun yi asara mai yawa.
In za a iya tuna wa, a bara, gwamnatin tarayyar ta shelanta cewa, ta ware naira biliyan goma sha uku da miliyan dari, musamman domin ta yaki halittun da ke illata amfanin gona, bayan an yi shuka.
A cewar gwamnatin, a cikin wadanan kudaden har da wadanda za a tallafa da su wajen dakile shigowar tsuntsayen cikin kasar nan, musamman a jihohin arewa.
Wasu daga cikin manoman, irin su, Malam Umaru Garba Shuni, wanda yana daya daga cikin maomnan da tsutsayen suka auka cikin gonarsa, ya sanar da cewa, tsuntsayen sun yi wa amfanin gona da ya shuka illa.
A cewar Malam Umaru, tsuntsayen sun shiga gonarsa, inda suka lalata masa amfani.
Shi ma wani manomi a kauyen, mai suna Alhaji Sambo, ya nuna cewa, kafin gwamnati ta kawo musu dauki wasu manoma a kauyen, na amfani da wani salo na gargajiya wajen korar tsuntsayen.
Alhaji Sambo ya ci gaba da cewa, lokacin da tsitsayen suka bulla gonanarsu sun yi kokarin korarsu daga cikin gonakinsu, inda ya kara da cewa, amma idan har tsuntsayen suka ji karar wasu abubuwan da manoman suke kada wa don su kore su daga cikin gonakinsu sai su gudu, haka kuma, suna yin amfani da zaren kaset na bidiyo wanda idan iska ta kada, sai tsuntsayem su fice daga cikin gonakin nasu.
Haka kuma, shi ma wani manomin mai suna Malam Murtala Gagadu ya bayyana cewa,a bara, tsuntsayen sun bulla a wasu yankunan Isa, da Sabon-birni, da Wurno, da Wammako.
Ya kara da cewa, hakan sai ya sa suka bukaci agaji daga hukumomin aiki gona a jihar da kuma tarayya.