Dan Haya Ya Ciji Leben Mai Gida Saboda Tambayar Sa Kudin Haya

Leben

Wani abu kamar wasan kwaikwayo ya auku a ranar Talata a wani kotu a inda mai gabatar da kara na ‘yan sanda ya nemi alkali da ya dauki hukunci mai tsauri kan wani dan haya da ake zargi da cizon leben mai gidansa saboda ya nemi da ya biya kudin hayar da yake binsa.

An tuhumi dan hayar, Ernest Ekeh da cin zarafi da kuma tayar da zaune tsaye na zaman lafiya a gaban Kotun Majistare ta Ejigbo da ke jihar Legas.

Mai gabatar da kara, Kenneth Asibor, ya bayyana cewa, kafin aukuwar wannan lamari, dan hayar ya ta yin barazanar maganin mai gidan, Matthew Kunle idan har ya kuskura ya nuna fuskarsa a kofar gidansa kan batun biyan kudin haya.

’Yan sanda sun ce, mai gidan ne ya sanar dasu lamarin wanda ya faru a yankin Igando da ke Legas. Suka ce, “Wanda ake zargin, ya hadu da mai gidan nasa ne a fusace a inda ya kama rigarsa ya daga shi sama ya buga da kasa kafin ya cije lebensa na kasa.

Mai gidan ya ce, “Bai cancanci a sake shi ba. Ina rokon ku da ku yanke masa hukunci mai tsauri don nuna misali ga sauran masu irin halinsa, wadanda suke ganin kamar sun fi karfin doka, kuma suke daukar doka a hannunsu.”

Wani dan sandan ya fadawa kotun cewa, dan hayar da mai gidan nasa sun dade suna samun matsala kan biyan kudin haya kuma sun yanke shawarar amfani da barkewar korona da kulle a matsayin uzuri. Mai gidan ya yi barazanar korar dan haya, lamarin da ya fusata dan hayar kenan ya aikata wannan laifi.

An kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda da ke Igando kuma an kama wanda ake zargin. Daga baya an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare da ke Ejigbo, Legas.

Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin. Mai gabatar da kara, Supol Kenneth Asibor, ya roki kotun da ta ba da ranar sauraren karar don bai wa ‘yan sanda damar tabbatar da cewa wanda ake karan da gaske ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Alkalin kotun, Mr. E.O. Ogunkanmi, ya bayar da belin Eke a kan kudi Naira 50, 000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Bugu da kari, Eke bai iya cika ka’idojin belin ba kuma an sake tura shi zuwa cibiyar gyara yayin da zai kammala cikakkun sharuddan belinsa.

 

Exit mobile version