Wani dan wasan kwallon kafa da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fadi ya mutu a lokacin da yake wasa a filin wasan kwallon kafa na Green Field da ke unguwar Lekki a Legas.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ne, ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.
- Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Titin Abuja Zuwa Lakwaja
- Mai Gida Ya Kashe ‘Yar Hayar Gidansa Da Wuka A Ondo
Kakakin ya ce jami’an ‘yansanda reshen Maroko ne suka kai bayanan ga rundunar jihar.
Ya ce dan wasan kwallon kafar mai shekaru 31 da ba a san shi ba, ya mutu da misalin karfe 6.30 na yamma a ranar juma’a.
An garzaya da marigayin zuwa Asibitin Ever Care da ke Lekki inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
“Bisa rahoton, tawagar jami’an tsaro sun ziyarci wurin wasan kwallon kafar da kuma asibitin da aka duba gawar tare da daukar hotuna.
“An ajiye gawar a dakin ajiye gawa domin gudanar da bincike.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji Hundeyin.
Jami’in ya shawarci jama’a musamman ‘yan wasa da su rika duba lafiyarsu akai-akai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp