Dan majalisar wakilan Nijeriya da ke wakiltar mazabar tarayya ta Egor/Ikpoba Okha a Jihar Edo, Jude Ise-Idehen, ya rasu.
Dan majalisar ya rasu ne a yau Juma’a da safe a sanadiyyar rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
- Da Dumi-Dumi: Gidajen Burodi Sun Tsunduma Yajin Aiki A Abuja
- Kungiyar Kwadago Za Ta Yi Zanga-zangar Wuni Guda Don Mara Wa ASUU Baya
Shugaban kwamitin yada labarai a majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya tabbatar da mutuwar amma kuma ya ce har yanzu majalisar ba ta san musabbabinta rasuwarsa ba.
Marigayin ya kasance dan majalisar jihar ta Edo, kafin daga bisani aka zabe shi zuwa majalisar tarraya a jam’iyyar PDP.
Ana ganin Idehen, mai shekara 52 wanda ya samu tikitin sake takarar kujerar tarayyar a zaben 2023, daman yana fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp