An kama wani sufeton ‘yan sanda a jihar Kaduna da laifin yunkurin kashe abokin aikinsa a Kafanchan da ke karamar hukumar Jemaa a jihar.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammed Jalige, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Yuni, 2023, a sansanin ‘yan sanda da ke Kafanchan, a lokacin da Sufeto Moses Paul ya yi yunkurin kashe abokin aikinsa, wani sufeto Simnawa Paul ts hanyar amfani da igiya ya shake wuyansa.
- Mataimakiyar Sakatare Janar Na MDD Na Ziyara A Kasar Sin
- Firaministan Sin Ya Gana Da Darakta Janar Ta WTO
Mutumin da lamarin ya shafa ap cewar kakakin ‘yan sandan, wasu ‘yan sanda biyu ne suka kubutar da shi saboda kukan da ya yi.
Jalige ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewar shi ne yunkurin kwace bindigar Sufeto Simnawa Paul yayin da za a gano dalilin daukar matakin karshe a cikakken bincike.
Ya ce, idan aka same shi da laifi, Paul zai fuskanci hukunci da shari’a.