Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa har yanzu fitaccen dan Ta’adda Ado Aleru, wanda masarautar Yandoto Daji ta jihar Zamfara ta yi masa rawanin sarauta a ranar Alhamis din da ta gabata, har yanzun yana cikin jerin sunayen wanda take nema ido-rufe.
Rundunar ta ce Alero ya kashe mazauna jihar Katsina 100.
- An Dakatar Da Sarkin Da Ya Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Sarauta A Zamfara
- An Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Sarauta A Zamfara
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani kan sarautar da aka baiwa shugaban ‘yan bindigar a jihar Zamfara.
Isah ya ce rundunar na tuhumar Aleru da laifukan da suka hada da kisan kai, ta’addanci, fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Ya kara da cewa, ana kuma neman Aleru da laifin kashe mutane sama da 100 a kauyen Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a jihar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a watan Yunin shekarar da ta gabata na neman Alero mai shekaru 47 da haihuwa a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, ruwa a jallo, inda ta daura kyautar Naira miliyan 5 – a mace ko a raye ga duk wanda ya kawo mata shi.