Dan takarar gwamnan Jihar Osun na jam’iyyar Labour Party, Lasun Yusuf, ya tsallake rijiya da baya, inda ya samu kubuta daga mutuwa biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai masa a gidansa da safiyar ranar Litinin.
Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai an kai masa harin ne a gidansa da ke Ilobu da ke karamar hukumar Irepodun a jihar wajen karfe 2:00 na dare.
- Hawan Nassarawa: Sarkin Kano Ba Zai Ziyarci Gidan Gwamnatin Kano Ba
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 18 A Zamfara, Mutane Sun Tsere Daga Gidajensu
Da ya ke ankarar da abin da ya faru da shi a shafinsa na Twitter, Yussuff ya ce, ‘yan bindiga sun yi ta harbi har a makwaftansa.
Ya ce, “Yanzu haka ‘yan bindiga suna cikin gidana suna ta harbe-harbe na tsawon lokaci ba kakkautawa..”
A lokacin da aka tuntubi kakakinsa Mista Oyewole Oladimeji, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp