Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Delta a ranar 18 ga Maris, 2023, Sheriff Oborevwori, ya tsallake rijiya da baya a kan hanyar Warri-Sapele.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Dennis Otu ya fitar, Oborevwori yana kan hanyarsa daga Sapele zuwa Osubi lokacin da lamarin ya faru.
- Birnin Beijing Zai Kara Yawan Lambunan Shakatawa
- Hukumar Kula Da Aikin Makaurata Ta Kasar Sin Ta Daidaita Manufofin Ba Da Iznin Shigo Kasar
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, 2023, tawagar dan takarar gwamnan PDP na jihar Delta, Rt Hon Sheriff Oborevwori, sun fuskanci mummunan hari daga wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba a tsakanin mahadar Elum da Okuabude a karamar hukumar Okpe ta jihar.
“Motar da aka shiga da shi da kuma motocin jami’an tsaro da ke makare da ayarin motocin na dauke da harsasai a lamarin da ya faru da misalin karfe 9:05 na dare.
“Ya tsira sakamakon shiga mota mai hana harsashi hudawa.
“Jajirtattun jami’an tsaronsa sun yi aiki tukuru, inda suka fatattaki maharan.”
Sanarwar ta kara da cewa “An kai rahoton lamarin ga ‘yansanda don ci gaba da bincike.”