Mai neman takarar kujerar gwamna a jihar Zamfara a inunwar jamiyyar PDP, Ibrahim Shehu, ya kalubalanci lashe zaben fidda gwani da Dauda Lawal Dare ya samu a zaben fidda gwani da PDP ta yi a kwanakin nan.
Shehu ya shigar da kara ne a gaban kotun tarayya da ke da zamanta a garin Gusau, inda ya yi zargin cewa, an tabka magudi a lokacin da aka gudaanar da zaben fidda gwani, ya kuma roki kotun da ta soke zaben don sake wani sabo.
- 2023: Atiku Ya Gabatar Da Gwamnan Delta, Okowa A Matsayin Mataimakinsa
- Gwamna Wike Bai Halarci Taron PDP Na Bayyana Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku Ba
A cikin karar da Shehun ya shigar ya hada da sunan shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben na fidda gwani Adamu Maina Waziri da shugaban PDP na jihar, Kanal Bala Mande, mai murabus.
Har ila yau, a cikin karar, ya kuma sa sunan hukumar zabe INEC da kuma sunan Dauda Lawal Dare
Alkalin kotun, Bappa Aliyu, ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Yuli saboda rashin zuwan wadanda ake karar a gaban kotun.