• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP A Kano Municipal, Da’awah Ya Rabawa Dalibai 500 JAMB

by Muhammad
3 years ago
Dalibai 500 'Yan Asalin Kano Municipal Da Suka Ci Gajiyar Tallafin Jarabawar JAMB Daga Hon Da'awah

Dalibai 500 'Yan Asalin Kano Municipal Da Suka Ci Gajiyar Tallafin Jarabawar JAMB Daga Hon Da'awah

Dan takarar majalisar tarayya na Jam’iyyar PDP a karamar hukumar birni, Hon. Injiniya Yusuf Abdullahi Da’awah, ya gwangwaje dalibai 500 ‘Yan asalin Kano Municipal da rabon Jarabawar shiga makarantun gaba da sinkandire ta UTME wacce aka fi sani da JAMB.

Hon. Yusuf Abdullahi Da'awah
Hon. Yusuf Abdullahi Da’awah

An gudanar da taron rabon jarabawar a yammacin ranar Asabar din nan 18, ga Febarairun 2023 a filin taro na kofar gidan Qadiriyya da ke unguwar Kabara mazabar Tudun Wuzirchi a karamar hukumar birni.

  • Da’awa Ya Kaddamar Da Shirin Mayar Da Yara 1300 Makaranta Da Rabon Kayan Karatu
  • Atiku Ya Kaddamar Da Makarantar Haddar Al-Kur’ani A Kano

A jawabinsa a wurin taron, Injiniya Da’awah, ya godewa Allah bisa wannan dama da ya samu ta daukar nauyin ba wa dalibai 500 JAMB a karo na bakwai bayan rabon Jarabawar NECO da aka yi a baya da rabon kayan makaranta ga ‘Yan Firamare da litittafai da jaka.

Dalibai 500 'Yan Asalin Kano Municipal Da Suka Ci Gajiyar Tallafin Jarabawar JAMB Daga Hon Da'awah
Dalibai 500 ‘Yan Asalin Kano Municipal Da Suka Ci Gajiyar Tallafin Jarabawar JAMB Daga Hon Da’awah

Da’awah ya yi wa daliban alkawarin cewa matsawar ya yi nasara a zaben da za a gudanar ranar asabar mai zuwa 25, ga Febarairun 2023 zai dauki nauyin karatunsu har su kammala karatu a Jami’o’in da suka samu gurbin karatu tare da samar musu da aikin yi bayan sun kammala karatun.

Dalibai 500 Da Suka Ci Gajiyar Tallafin JAMB Daga Hon Da'awah Lokacin Da Suke Karbar Horo Kan Jarabawar
Dalibai 500 Lokacin Da Suke Karbar Horo Kan Jarabawar JAMB

Da’awah ya ce, rabon jarabawar ba siyasa a ciki don kuwa babu wanda ya sani cikin daliban, an yada sanarwar ne kawai ta kafafen sada zumunta, su kuma daliban sun cike aka kuma dauke su bisa cancantarsu.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

Yusuf Da’awah ya yi alkawarin daukar nauyin yi wa daliban horo kan yadda za su rubuta jarabawar ta JAMB, ya kuma bukaci sauran Jama’a da su yi koyi da wannan tsarin don tallafar ‘ya’yan talakawa.

A nasu jawabin a wurin taron, wasu cikin daliban da suka ci gajiyar shirin, Umar Muhammad da Zainab Hassan Yahaya, sun godewa Da’awah bisa kokarinsa na bayar da tallafin karatun ga dalibai marasa karfi da addu’ar Allah ya kara daga darajarsa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 
Labarai

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

October 14, 2025
Kotu
Manyan Labarai

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Next Post
Ta Yaya Aka Samu Nasarar Kiyaye Rayuka Da Lafiyar Al’ummar Sinawa Daga Cutar COVID-19?

Ta Yaya Aka Samu Nasarar Kiyaye Rayuka Da Lafiyar Al’ummar Sinawa Daga Cutar COVID-19?

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

October 14, 2025
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

October 14, 2025
Kotu

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

October 14, 2025
Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

October 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

October 14, 2025
Asuu

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.