Tsananin fama da yunwa da fatara gami da rashin lafiya sun sanya wani dan shekara 30 a duniya rataye kansa har lahira a makon jiya a cikin wani gida da yake haya a kauyen Ditladi a Kasar Botswana.
Dan asalin kasar Zimbabwe da aka yi amannar na zaune a kasar Botswana ta haramtacciyar hanya, an ce ya jima yana korafin matsalolin rayuwa sun masa katutu wadanda har suka kaishi ga kashe kansa.
- Tsoma Baki Da Lalata Tsarin Samar Da Kayayyaki Da Amurka Ke Yi Bai Samu Karbuwa Ba
- Nijeriya Na Iya Fuskantar Karancin Abinci A 2023 –IMF
A cewar Kwamandan tashar Tonota, Oteng Ngada, mutumin ya fada wa abokansa, shi kam zai kashe kansa kawai saboda matsalolin sun masa yawa kuma zai yi hakan ne don neman hutu.
“Ya yi korafin talauci domin bai da komai da zai ci don haka shi bai ga wani dalilin cigaba da rayuwa ba,” a cewar Ngada.
“A lokacin da ya ke cikin dakinsa wajajen karfe 1200 mai kula da gidan hayarsu ya lura gidan ya yi duhu sosai wajajen karfe 2050. An yi ta kwankwasa masa kofa babu amsa, da mai kula da gidan hayar ya shiga sai ya ganshi kawai ya rataye kansa daga saman gidan.”
Ngada ya kara da cewa, iyalan mamacin da suka koma Zimbabwe an sanar musu halin da ake ciki.
“Gangar jikinsa (gawa) har yanzu na dalinnadana gawarwaki na Nyangabgwe.”