Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya rattaba hannun kan wata yarjejeniya da gwamnatin Jihar Niger na kafa kamfanin yin suga a Jihar wanda zai Lakume Naira Bilyan 166.
Aliko Dangote yace, kamfanin sugar zai samarwa matasa guraben aikin yi kimanin 15,000 inda ya nuna cewa a karkashin yarjejeniyar kamfanin zai rika noma rake a filin da aka kebe masa mai fadin hekta 16,000 a karamar hukumar Lavun.
Dangote ya kara da cewa, gina kamfanin zai kara samarwa ‘yan Nijeriya ayyukan yi.