Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa NPA Abubakar dantsoho ya yi kira ga masu zuba hannun jari, da suba jarinsu a Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasar.
Ya bukaci masu zuba hannun jarin da yi amfani da tsarin EPT na Hukumar na sauwake yin kasuwanci, musamman wajen fitar da kaya zuwa ketare.
- NPA Da Cibiyar PEBEC Sun Kulla Hadakar Samar Da Saukin Kasuwanci A Tashoshin Jiragen Ruwa
- Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
A cewarsa, yin amfani da wannan tsarin zai kara taimakawa wajen yin gasa kan kayan da ake sarrafawa a kasar domin kai wa kasuwar duniya.
Shugaban ya bayyana haka ne, taron baje koli kasa da kasa da Cibiyar Kasuwancin, Masana’antu, Ma’adanai da Aikin Noma ta jihar KADCCIMA ta shirya a kwanan baya.
“Tsarin na EPT an samar da shi ne, domin a samar da saukin hada kaya da tura su a cikin sauri, musamman ta hanyar yin amfani da fasahar zamani a Tashoshin Jiragen Ruwan,”. Inji dantsoho.
Kazalika, aikin bunkasa hada-hadar kasuwanci da Gwamnatin Tarayya ta kirkiro da shi wato NSW, zai bai wa masu ruwa da tsaki damar gudanr da hada-hadar kasuwanci ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.
kokarin da Hukumar ke yi na daukaka tsarin na EPT, zai kasance hanyar lalubo da mafita kan dogon shigen da ake da shi, na gudanar da hada-hadar kasuwani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp