Darajojin Manzon Allah (SAW) Da Suratul Fat’hi Ta Tattare (II)

Darajojin

Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) “Mu muka aiko ka (ya Rasulallahi a matsayin) mai shaida (ga al’ummarka) kuma mai bushara, sannan mai gargadi (Sai ya zamo tun daga kan Annabin da duk al’ummarsa) ku yi imani da Allah da Ma’aikinsa. Kuma ku girmama shi sannan ku girmama shi dai. Ku yi tasbihi ga Allah; safe da maraice. Ka ga wadannan da suke mubaya’a da kai; da Allah suka yi (mubaya’ar), Hannun Allah ne a kan nasu (yadda ya dace da Allah). Duk wanda ya warware wannan mubaya’a; kansa ya warware wa (kai dai ya Rasullallahi Allah zai taimake  ka). Duk wanda ya cika wa Allah abin da ya yi alkawari, Allah zai ba shi lada mai girma”.

Wadannan ayoyi tun daga farkon surar ta Fat’hi har zuwa wurin da Allah ya ce masu mubaya’a da Annabi sun yi ne da Hannun Allah (yadda ya dace da shi SWT); sun kunshi bayani ne a kan fifikon Annabi (SAW) da kirari gare shi da bayyana girman matsayi da darajarsa a wurin Allah. Da irin ni’imar da Allah ya yi a gare shi (SAW) da abin da siffantawa ma zai zama takaitawa ne a gare shi (SAW) – ballantana ma a ce wani ya kai karshe har ya ketare iyaka.

Allah mai girma da daukaka (a farkon surar) ya fara ne da sanar da Annabi (SAW) abin da ya hukunta a gare shi na daga hukunci mabayyani cewa Allah ya dora shi a kan makiyansa. Allah ya bayyana addinin Annabi (SAW) ya cika ko ina, yau ina su Abu Jahli? Allah ya rinjayar da Annabi a kan makiyansa da daukakar kalmar Manzon Allah (SAW) da Shari’arsa. Duk wadannan sun tatttaru ne a cikin fadin Allah (farkon surar) cewa shi Annabi (SAW) abin gafartawa ne a gare shi (duk abin da ya aikata na barin tarku aula), ba wanda za a rika ne da wani laifi ba, ba wani abu da zai yi nan gaba kuma a ce an rike shi da laifi.

Wani sashe na malamai ya ce, wannan yana nufin an gafarta masa ne (SAW) idan da ma akwai wani abu da ya kasance (na laifi) da abin da ma bai kasance ba da zai zo nan gaba, Allah ya gafarta masa. Sai mu lura a nan, duk da Allah ya ba Manzon Allah (SAW) garanti cewa an yafe masa (abin da ya yi a baya da wanda zai yi a gaba) amma Manzon Allah bai aikata wani abin assha ba. Shi ma Manzon Allah haka ya din ga yi wa wasu Sahabbansa garanti, yana fadin wane dan aljanna ne, wane da aljanna ne. Kuma su ma ba a ga suna aikata wani abin assha ba. Manzon Allah (SAW) ya ce duk ‘Yan Badar (wadanda suka halarci yakin Badar) Allah ya gafarta musu, duk abin da suka aikata ba za su shiga wuta ba, to kuma ba a ga wani Dan Badar ya yi shirka da Allah ko ya aikata wani laifi da za a iya cewa na assha ba ne.

Malamai sun ci gaba da bayanin cewa abin da ayar (ta farkon surar) take nufi, shi ne (ya Rasulallahi SAW) kai abin gafartawa ne. Malam Makki ya ce Allah ya sanya baiwa sababi ce ta gafara, duka da baiwar da gafarar daga Allah ne wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi. Bayan baiwa, darajantawa ne Allah ya ba Annabinsa. Sannan Allah ya ce zai cika ni’imarsa ga Annabi (SAW). Malamai suka ce meye cikar ni’ima ga Annabi (SAW) da Allah yake nufi? Suka ce ita ce kaskanta makiyansa (komai karfinsu na kudi da mulki) su dawo a karkashinsa. Kila kuma malamai suka ce cikar ni’imar tana nufin Allah zai bude masa Makka (Fatahu Makkata), ya so shiga sun hana shi sun ce sai dai ya dawo badi, to bari wata rana garin zai zama nasa, wand ya ga dama zai bar shi ya zauna a garin; wanda bai ga dama ba kuma ya kore shi kuma ya koru (SAW). Tana kuma nufin Allah zai bude wa Manzon Allah (SAW) Da’ifa. Kila kuma ma’anar cika ni’ima ga Manzon Allah (SAW) tana nufin Allah zai daga ambatonsa a nan duniya. Ba yanda za a yi ambaton Manzon Allah ya gushe, ba wanda yau a duniya zai ce bai san ambatonsa ba. Ga shi nan duk kiran sallah biyar sai an fadi sunansa kuma da karfi cikin daga murya, bayan sauran wuraren da ake ambatonsa kamar su tahiya da sauransu. In dai za a ambaci Ubangiji to sai an hada da Bawansa (Annabi SAW).

Allah zai taimake ka, Allah zai gafarta maka (ya Rasulallah SAW). Sai Allah ya sanar da shi (SAW) cikar ni’imarsa a gare shi ta hanyar kaskantar masa da girman makiyinsa, da bude masa mafi soyuwar garuruwa a gare shi (Makka), duk Allah ya bude masa. Haka nan Allah ya nuna masa zai bude masa Hira da Sham da Mada’in da Rum duk gabadaya ya fada wa Sahabbansa. Allah zai daukaka ambatonsa da shiryar da shi tafarki madaidaic, tafarkin da zai kai (mutum) zuwa Aljanna da arzikin lahira da taimakonsa, taimakon da ya zama mabuwayi da baiwar Allah ga al’ummarsa. Bayan ni’imar a kan Annabi (SAW), Allah Ta’ala ya kuma faranta wa Annabi rai a cikin al’ummarsa Muminai wanda ya natsar da zuciyarsu da natsuwa wanda Allah ya sanya a cikin zukatansu. Duk Mumini sai ka ga zuciyarsa a natse, za ka ga yana yin ayyukansa cikin hankali da natsuwa, amma duk wanda ba haka ba, sai ka gan shi a cikin tashin hankali, ko karatu zai yi sai ka ji yana yi a cikin tashin hankali kai ka ce sakon da yake isarwa da fada aka aiko, misalin irin wannan kamar kare ne, in ka bige shi ko ka bi shi da gudu zai yi haki; haka nan idan ka kyale shi yana hutawa duk dai za ka ga yana haki, Allah ya kiyaye mu. Mutum ya zamo yana cikin natsuwa.

Allah ya kuma yi wa (Muminan) bushara da abin da yake gare su a wurin Ubangiji. Duk Musulmi in dai ya yi imani (La’ila ha illallahu Muhammadur Rasulullah SAW), sauran abubuwa suna da sauki, zai samu Rahamar Allah. Komai laifin da Musulmi zai yi idan ya mutu ba za a ce yana wuta ba, sai dai a ce ya tafi Mashi’ar Allah, idan Allah ya ga dama ya azabtar da shi, idan kuma ya ga dama ya sa shi a rahama. Allah yana cewa mece ce ribar da zai ci idan ya yi muku azaba in dai kuka yi imani kuka yi godiya? Mutum ya yi imani da Allah iya kokarinsa, Allah Ta’ala zai gafarta masa, ya yarda da Allah; ya san Allah alheri ne ya yi nufi da shi, ya sa dadi a zuciyarsa; ba ya dinga yi wa Allah mummunan zato ba. Ai ka ga ma a karatunmu na baya, Allah ya ce yana mana bushara muna da wata ajiya a wurinsa, ajiyar shi ne Annabi Muhammadu (SAW). Kowane Musulmi ya yi bishara, ya san bayan imaninsa na Musulunci, bayan ibadarsa, yana da wata ajiya a Bankin Allah, shi ne Annabi Muhammadu (SAW), idan ka zama kana da Annabi (SAW) a lahira wannan babban alheri ne; ya ishe ka.

Exit mobile version