Darajojin Manzon Allah (SAW), Darasi Na Bakwai:

Manzon Allah

Siffofin Manzon Allah (SAW)

‘Yan’uwa masu karatu da ke bibiyarmu a wannan shafi mai albarka assalamu alaikum. Kafin mu shiga sabon darasinmu na yau, za mu dan yi bitar karshen darasinmu na makon jiya domin a fahimci karatunmu na yau da kyau.

Ka sani ya kai masoyin wannan Annabi mai girma, cewa dabi’un kyau da na cika a cikin Dan’adam sun kasu gida biyu. Na daya, Larurar Dan’adam ta duniya, misali tsawo ko gajarta, kyawu ko muni, karfin hankali ko nutsuwa, fasahar harshe, buwayar kabila, girman dangi, numfashi, rashin lafiya, da sauransu. Sai kuma dabi’u wadanda ake gode wa mai aikata su, ya kusanta shi izuwa ga Allah matukar kusanci. Kason farko, halittar Allah ce a jikin Dan’adam ba aikata ta ake yi ba dole ce tsarin halittar jikinsa, kaso na biyu kuma aikata su ake yi, mutum ke nemo wa kansa, misali hakuri.

Sai kuma kashin da ya kubuta a na Farko da na Biyu: shi ne wadanda larurar rayuwa ta zo da su kamar wurin kwana, cin abinci, yin bacci, tufafinka, auratayya, dukiyarka, alfarmarka. Wadannan dabi’u suna iya zama na lahira in Dan’adam ya yi nufin aiki da su don Allah, kamar ya ci abinci don jikinsa ya yi karfi, ya iya yin Ibada, ya yi aure don bin umarnin Annabi kuma ya kauace wa zina, ya yi bacci don ya iya fita neman halal, ya sa tufafi don rufe tsaraici da kuma gode wa falalar da Allah ya yi masa, ya yi aikin da zai kare mutuncinsa. Duk yin wadannan dabi’u don neman karfafuwa da jikinka ka yi ibada za su kai ka ga lahira.

Sai kuma dabi’un da suke da alaka da lahira wadanda Dan’adam yake neman su da kansa, kamar ka zama mai Addini, neman Ilimi, Hakuri, Juriya, Godiyan Allah, Adalci, Zuhudu, Kankan da kai, Rangwame, Kamewa, Kyauta, Sadaukantaka, Kunya, Mutunci, Nutsuwa, Jinkai, Kyakkyawan ladabi, Zaman lafiya da mutane, da sauransu. Wadannan dabi’u in an tattare su wuri guda su ake kira da ‘Husnul Kuluki’. Wadannan dabi’u na aikin lahira za su iya kasancewa na halittar mutum, a ce haka aka halicce shi da ita. Wasu mutane kuma za ka ga ba su da daya daga cikin wadannan dabi’u, haka aka halicce su. Shi da kansa, tunda ya ji an ce dabi’u ne masu kyau, sai ya nemo wa kansa.

Wadannan dabi’u na aikin lahira za su iya kasancewa na halittar mutum, a ce haka aka halicce shi da ita. Wasu mutane kuma za ka ga ba su da daya daga cikin wadannan dabi’u, haka aka halicce su. Shi da kansa, tunda ya ji an ce dabi’u ne masu kyau, sai ya nemo wa kansa.

Haka kuma wadannan dabi’u na aikin lahira da muka fada a baya, za su iya kasancewa na aikin duniya idan aka aikata su ba don Allah ba. Sai dai cewa ko dai mutum bai nufi aikin Allah da ita ba, dabi’u ne masu kyawo wacce take jawowa a yabi mutum da ita, sabida dabi’u ne kyawawa, kuma babu yadda za a yi Dan’adam ya gane cewa ba a nufi Allah da ita ba sabida a zuciya take, sai dai kuma in aikinsa ya nuna. Amma dole za a yabi mutum da kyawawan dabi’unsa, a ce wane mai hakuri, mai Ilimi, mai nutsuwa, da sauransu. Dukkan wannan dabi’u kyawawa ne kuma madaukaka ne, in ji masu hankali.

Masu hankali suna cewa “a ce kana da dabi’u kyawawa, ya fi a ce ba ka da su” duk da yake an sami sabani a cikin maganar tasu kan cewa wai mai ya jawo dabi’un suka zama masu kyawo da daukaka.

Yanzun bara mu juya akalar zancenmu zuwa magana kan dabi’un manzon Allah (SAW na girma da kyau.

Imam Alkadi Iyad ya ce “ idan dabi’un cika da na kyau suka zama daya daga cikin abin da muka fada a baya ne za mu ga daya daga cikinmu yana daukaka da daya daga cikin wadannan dabi’u: Addini, Ilimi, Hakuri, Juriya , Godiya, Adalci, Zuhudu, Kankan da kai, Afuwa, Kamewa da sauransu”, mutum yana daukaka in ya yi shuhura da daya daga cikin wadannan, za ka ji ana cewa wane mai hakuri ne, ko mai kyauta ne. Za ka ga mutum ya daukaka idan Allah ya ba shi daya tak daga cikin wadannan dabi’u, in kuma Allah ya hada masa biyu sai daukakarsa ta karu. Kuma hakan a kowane zamani, za ka ga ana girmama shi sabida dan gidan wane ne, ko a ce mai kyawun jiki ne, mai Ilimi ne, sadauki ne, ka ga girmansa ya daukaka, har ana buga misali da shi.

Daga cikin mutanen Jahiliyya har yanzu ana buga misali da wasu, in kyauta ne a ce akwai Hatimud Da’i, sadaukantaka akwai Antara dan Shaddadu, akwai abubuwa da dama.

Wannan buga Misali da abin da mutum ya daukaka da shi, hakan yana tabbata a zukatan mutane matukar zamani mai nisa. Wani mai wani hali da ya yi shuhura da shi, ya dade da mutuwa amma har gobe ana buga misali da shi sabida shuhura da daya daga cikin kyawawan dabi’u.

To meye zatonka ga girman darajar da wadannan dabi’u duk ta tabbata a gare shi, Na halitta da duk na dabi’u duk sun taru a cikinsa? Kai, abubuwa na kyawon dabi’u duk sun tabbata a gare shi wanda ba za a iya kididigewa ba, ba a isa a iya tsururun abin da yake dashi ba, ba a isa a iya yin wata dabara da za a iya samun abin da yake gare shi ba sai da kebantar Ubangiji Madaukaki. Allah ne mai bayarwa kuma shi yaba wa Annabi Muhammad (SAW). To wa ya isa ya san girman darajar wanda duk wannan dabi’un suka tabbata a gare shi na daga fifikon Annabta? Ita annabta ba a neman ta da yin wani aiki, baiwa ce daga Allah; Fifikon Manzanci da Badadantaka, Masoyin Allah ne, zababben Allah ne, Allah ne ya yi tafiyar dare da shi (Isra’i), ya ga Allah da Idonsa, ya kusanta da Allah, ana masa wahyi.

An ba shi ceto, an ba shi madaukakiyar daraja, an ba shi mukami abin godewa (Makamul Mahmudi). An ba shi buraka ta zama abin hawansa, an yi Mi’iraji da shi, an turoshi i zuwa jar fata da bakar fata, ya yi wa Annabawa da Manzanni limanci, shi zai yi shaida tsakanin Annabawa da Ummatai duka, shi ne shugaban ‘ya’yan Adam duka, shi ke rike da Tutar Godiya (Liwa’ul hamdi), shi ne mai yi wa mutane bishara da gargadi, shi ke da babbar daraja a wurin Ubangiji mai Al’arshi, duk Mala’iku masu biyayya ne a gare shi a can. Shi ke da Amana da Shiriya, kuma Rahama ne ga duk halitta, shi aka bawa yarda, shi aka ba damar yin tambaya, shi aka ba Alkausara, shi aka ba cikar Ni’ima da rangwame daga abin da ya gabata da wanda ya jinkirta. An dauke masa duk wani nauyi, an yalwata masa kirji, an daukaka ambaton sa, an ba shi buwayar taimako, an saukar masa da nutsuwa, an karfafe shi da Mala’iku, an ba shi Alkur’ani da Ilimin cikinsa, an ba shi Shari’a da Ma’arifa, an ba shi Sab’ul Masani, an tsarkake al’ummarsa.

Shi ne wanda Allah da Mala’ikunsa suke yi wa Salati, an bashi ‘yancin yin hukunci da abinda Allah ya nuna masa su kuma sauran Annabawa sai abin da aka saukar musu a littafinsu. Allah yana rantsuwa da sunansa, Allah yana amsa addu’arsa, shi yake magana da sandararrun abubuwa da dabbobi, yana raya matattu, yana jiyar da kurame magana, ruwa ya bubbugo daga hannunsa, dan abu kadan yanzu ya zama mai yawa a hannunsa, an tsaga  masa Wata, ya maido da Rana. Allah ya yi mai Nasara, ya amintar da shi a duk inda zai nufa, Allah ya nuna masa gaibi, Allah ya tsare shi daga sharrin mutane, ba wanda zai iya iyakance ilimin abubuwan da Allah ya ba shi sai shi Allah wanda ya ba shi kuma ya Fifita shi da su, kuma babu wani Ubangiji sai Allah, sannan ka dada da abin da Ubangiji ya tanadar masa a ranar Lahira na daga masaukan daraja da martabobin arziki a Aljanna da ganinsa na Rabbul Izzati, wacce hankali ya gaza kaiwa wurinta.

Idan Muka koma bangaren magana kan siffofin Annabi Muhammadu (SAW) na halitta, dukkan mutane daga masoyansa da makiyansa duk sun hadu cewa shi ya fi kowa girman daraja da daukaka kuma shi ne mafi cikar kyawawan dabi’u da siffofi.

Idan ka yi dubi ga siffofin, za ka same su ba tsururi ake yi a samo su ba, kuma za ka tarar Annabi shi ne mafi cikar siffofi gaba daya sannan ya tattare dukkanta. Za ka ga wani kyawun fuska gare shi, wani kyawun jiki gare shi, wani kyawun gabbai gare shi amma Annabi shi ya tattare dukkansu kuma babu sabani a cikin wadanda suka tattaro hadisan Siffofinsa da dabi’unsa.

Siffar Annabi da kyawonsa kowacce gaba ta dace da inda aka ajiye ta. Yana daga cikin Hadisin da aka karbo daga Sayyidina Ali da Anas bin Malik Kadimin Manzon Allah (SAW) da Abi Hurairata da Barra’u da Sayyada A’isha Uwar Muminai da dan Abi Halata – dan Sayyada Khadijah uwar Muminai da Abi Juhaifat Da  Jabir dan Samurata da Ummu Ma’abadin da Abdullahi bin Abbas da Abis Suhaili da Kuraimu bin Kafitin da Hakimu bin Hizamu da sauransu.

Manzon Allah SAW ya kasance mai hasken launi ne, mai farin ido, mai bakar kwayar ido ko kuma a ce mai gaza-gazan ido, mai yalwan ido, sannan akwai ja-ja a cikin farin idon, mai yawan gashin ido, mai hasken goshi, mai zananniyar/hadaddiyar gira, mai kewayayyiyar fuska, mai yelwar goshi, mai kaurin gemo, mai daidaiton ciki da kirji, mai yalwan kirji, mai girman kafadu, mai girman kashi, mai girman damtse, mai yalwan tafi da digadigi, mai tsawon yatsu, mai tsawo ne,  mai sakakken gashi, idan ya bude baki zai yi dariya sai ka ga haske kamar walkiya kuma kai ka ce hakoransa kamar kankara, mai madaidaicin wuya, mai daurarren jiki.

Sahabi Barra’u yana cewa “ban taba ganin mutum mai gashin kai da yawa har ya zuba a gadon baya ba a cikin jajayen kaya wanda ya fi Annabi Kyau ba (SAW).”

Exit mobile version