A wata ziyarar aiki da na yi a tsakiyar watan Agusta, direbana a Jihar Taraba ya shafe kusan fiye da rabin tafiyar zuwa masaukin mu yana magana a kan Gwamnan Zamfara, wanda kuma shi ne mai gidana.
Direban ya ambaci cewa gwamnan shi ne mafi karancin shekaru a cikin gwamnoni, mutum na musamman, wanda kuma kuma bai gajiya da aiki. Na tasa kunne ina saurare saboda mun saba jin irin wadannan dadadan maganganu game da Dauda Lawal.
- Gwamnatin Katsina Ta Sassauta Dokar Hana Yawon Dare A FaÉ—in Jihar
- Gwamna Dauda Ya Ziyarci Yankunan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Gummi
A yau, 2 ga Satumba, 2024, mai gidana, wanda a kodayaushe ake yawan ganinsa a matsayin matashi, yana cika shekara 59 a duniya. Tun a makon da ya gabata nake ta zurfafa tunani kan abin da zan rubuta a matsayin karramawa ga Gwamna Dauda Lawal. A baya na yi rubutu da yawa a irin wannan rana, amma wadanda na fi so a zuciyata fiye da kowanne su ne masu taken ‘Dauda Lawal: Mutuminmu, Burin Al’umma’ da ‘Dauda Lawal Din Da Na Sani’.
A ranar 29 ga Mayu, 2023, wani sabon babi ya bude a rayuwarmu yayin da Dauda Lawal, mutumin da muka sani a matsayin mai zaman kansa, ya karbi kujerar gwamnan jha. A yanzu ya dauki nauyin mulkin jihar da ke fama da matsalar ’yan bindiga, koma-baya a bangaren harkokin ilimi, kiwon lafiya, da walwalar ma’aikatan gwamnati, da dai sauran muhimman batutuwa.
Tsawon shekaru kafin 29 ga Mayu, 2023, Dauda Lawal ya kasance mai gidana – mutum ne da ya saba kiran kowane ma’aikacinsa ‘dan uwana.’ Babu wani mukami a duniya da zai iya canja karamci da mutuntakar Dauda Lawal.
Duk da cewa ranar 2 ga watan Satumba ba ranar tattauna dimbin nasarorin da Gwamna Dauda Lawal ya samu ba ne a matsayin gwamnan Zamfara a cikin shekarar da ta gabata, domin an yi ta yada su a kafafen yada labarai.
Yau rana ce da ta ya fi dacewa a bayyana salon jagoranci da halayen Gwamna Lawal. Idan har kana da abubuwa da yawa da za ka bayyana, zai fi dacewa ka takaita, domin wasu bayanai na bukatar littafi ne (ina aiki a kan hakan. Littafi ne da zai wayar da kan mutane da dama).
Mai gidana Dauda Lawal mai saurare ne. Yana da salon da Shugaban Amurka na 30, Calbin Coolidge, yake cewa, ‘Duk nagartaccen mutum ya kasance mai saurare.’
Ga Margaret J. Wheatley, ta ce, saurare yana matsar da mu kusa da al’umma kuma yana taimaka mana mu zama cikakkun mutane, maau lafiya, kuma masu hankali. Rashin sauraro yana haifar da rarrabuwa, kuma rarrabuwa shi ne tushen duk wani wahala.
Mai gidana, Dauda Lawal, Allah Ya yi masa da kusan komai. Na sha ji yana fadin cewa da a ce an ba shi damar tsara rayuwarsa, ba zai iya tsara ta da dimbin ni’imomin da Allah Ya yi masa ba.
Mai gidana shi ne shahararre Dauda, wanda ya kasance abin yabo a gari. Sau da yawa mutane sukan yi hasashen da bai daidai ba wajen auna dukiyarsa, bk Naira kadai ba, har da dalar Amurka. Mai kamala da kyan hali, Dauda Lawal a kullum yana fitowa tamkar matashi mai shekaru arba’in da haihuwa saboda ya san saka sutura, hakkun!
Ba kamar sauran mutane masu irin mukamin sa ba, ya ba ya jijinda kai. Mai gida na, mai tawali’u ne, mai janyo mutane kusa da shi, karbar al’umma. Yana karfafa ma’aikatansa sosai don su fadi ra’ayoyinsu. Yana shirya taruka na kai-tsaye tare da kananan jami’ai, masu tsaron kofa, direbobi, masu kula da tsirrai, da masu goge-goge don sauraron ra’ayoyinsu game da yanayin aiki da duk wata damuwa da suke da ita.
Kasancewar mai gidana Dauda Lawal mai sanin makamar aiki ne, ya san duk abin da ke gudanar a cikin gwamnatin sa. Kwamishinoni, masu ba da shawara, da sauran manyan jami’an tawagarsa suna taka tsantsan a cikin ayyukansu domin yana da masaniya a kan komai. Kofofinsa a bude suke, kuma ana iya samun wayarsa a koda yaushe (Ina tsammanin ma kusan kowa yana da lambar wayarsa). Gidan Dauda shi ne mafi saukin shiga idan aka kwatanta da gidajen wasu gwamnoni.
Dauda Lawal mai kyauta ne mai fara’a. Shi ya sa mutanen da suka fi shan wahala a gwamnatinsa su ne wadanda ke fama da matsalar ‘Sadistic Personality Disorder’ (kadan ne ma, idan akwai). Akwai mutaben da a kullum su na cikin fushi da bakin ciki saboda mai gidana Dauda Lawal, yana jin dadin bayarwa, taimako, da sanya murmushi a fuskokin al’umma. Wani abu mai dadi shi ne babu wanda zai iya tilasta masa ya yi abin da ba daidai ba (ma’ana, ba a masa abin da Bahaushe ke cewa ‘Ba a mugun sarki sai dai mugun bafade’). Babu! Kar ka yarda wani ya yi maka karya.
Idan kana son ka bata garrin ka a gaban Dauda Lawal, ka tunkare shi da tsegumi da ’yan kananan maganganu. Yana daraja ikhlasi kuma ba ya son fasikanci da rashi gaskiya. Yayan yawan cewa ba ya son aiki ‘kiya’. Kwararre ne wanda ke da kwarawa sosai a harkokin sa.
A duk lokacin da na shafe tare da shi, na san cewa mai gidana yana saurin fushi da mutanen da ba su da tsafta. Yana son tsafta sosai kuma yakan jaddada muhimmancin goge hakora da yin amfani da tuaren jiki na ‘deodorants’ da turaren kaya mai kamshi mai dadi ba mai hawa kai ba. Bai zai yiwu a kusanci shi da warin baki ko warin jiki ba; abu ne da zai masa dadi ba.
Yayin da ka ke cika shekaru 59 a daniya a yau, ina so ka sani cewa mutane da yawa su na sha’awar salon ka kuma suna girmama ka. Ka samu mutuntakar ka wajen ayyukan taimako a bangaren kamfanoni masu zaman kansu, kuma yanzu ka kafa tarihi a matsayinka na jagoran tawagar ceto Zamfara. Barka da Ranar Haihuwarka, Gamjin Zamfara!
Sulaiman Bala Idris shi ne Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara