Connect with us

LABARAI

Daukar Aiki: NIS Ta Gargadi Jama’a Su Ankare Da Tarkon ‘Yan Damfara

Published

on

Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta gargadi ‘Yan Nijeriya su guji mu’amala da wani shafin intanet da aka bude na damfara da sunan daukar aiki a hukumar wanda ta ce sam ba ta da alaka da shi kwata-kwata.
Hukumar ta yi gargadin ne a wata sanarwar manema labarai da ta fitar ta aike wa LEADERSHIP A Yau kwafenta daga shugabanta, CGI Muhammad Babandede MFR.
Sanarwar ta kara da cewa, “an ankarar da Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa Muhammad Babandede MFR game da wani shafin intanet na damfara da macuta suka samar da sunan daukar aiki a hukumar wanda ake ta rarrabawa a shafukan walwala na zamani (social media) da nufin damfarar ‘Yan Nijeriyan da ba-su-ji-ba-ba-su-gani-ba; makudan kudi.
“Hukumarmu ta sha gargadin jama’a a kan su ankare da ire-iren wadannan ‘yan damfara kuma har yanzu ba ta gaji ba tana sake gargadi ga ‘yan kasa na gari su guji hulda da wannan shafi na daukar aiki na boge wanda kwatakwata ba shi da alaka da NIS ballantana a ce an wallafa a shafinta na ainihi”.
NIS ta kara da cewa babu ko kwabo da ake caja wajen daukar aikinta, don haka tana shawaratar jama’a su yi watsi da shafin na ‘yan damfara domin kauce wa fadawa tarkonsu. Inda ta kara da cewa, “A koyaushe NIS za ta rika sanar da shirinta na daukar aiki a hukumance a sanannun jaridu na kasa da sauran kafafen yada labaru domin janyo hankulan al’umma a kan lamarin,” in ji sanarwar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: