Hannu na daga cikin sassan jiki da ake yawan amfani da su a ayyukan yau da kullum. Saboda haka, suna bukatar kulawa ta musamman domin fatar hannu ta kasance cikin tsafta, laushi da kyau. Yawan wanke hannu, amfani da sabulu mai karfi, ruwan zafi da wasu sinadarai na iya sa fata ta bushe.
Hanyoyin kare hannu daga bushewa:
1. Amfani da sabulu mai laushi:
A rika amfani da sabulu ko cleanser mai laushi, musamman wanda ba shi da kamshi mai karfi, domin kada ya cire danshin fatar hannu.
2. Shafa man kula da fata:
Bayan an wanke hannu, a shafa moisturizer mai laushi domin taimaka wa fata ta rike danshi kuma ta kasance cikin laushi.
3. Guje wa ruwan zafi sosai:
Yawan wanke hannu da ruwan zafi na iya kara busar da fata. Saboda haka, ana so afi amfani da ruwan dumi ko ruwan da bai yi zafi sosai ba.
4. Kare hannu yayin aikin gida:
Lokacin wanke-wanke ko amfani da kayan tsaftace gida, yana da kyau a kare hannu daga sinadarai masu karfi domin kada su jawo bushewa ko kaikayi.
5. Kada a yawaita gogewa:
Bayan an wanke hannu, a busar da shi a hankali da tawul mai laushi, ba tare da gogawa da karfi ba.
6. Kula da farce:
A rika tsaftace farce da yanke shi a kai a kai, domin tsaftar farce na daga cikin kyakkyawar kulawar hannu.
7. Shan ruwa:
Shan isasshen ruwa da cin abin ci mai gina jiki na taimakawa wajen kula da lafiyar jiki da fata.
8. Kula da hannu lokacin sanyi:
Lokacin da iska ta busa wato lokacin bazara, a kara kula da hannu ta hanyar amfani da moisturizer domin rage bushewar fata.
Kula da hannu ba wai don kwalliya kawai ba ne, har ila yau yana daga cikin kula da lafiyar fata. Don haka, ki sanya tsaftar hannu, amfani da moisturizer da kare fata daga sinadarai masu karfi cikin tsarin kulawar jikinki na yau da kullum.














