Kocin Manchester United Ruben Amorim ya bayyan cewar Kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Everton David Moyes ba mutum ne wanda za a raina iyawarshi a harkar kwallon ƙafa ba, David Moyes ya na yin aiki mai kyau na farfado da Everton fiye da yadda na ke yi cikin ƙanƙanin lokaci a Old Trafford inji Amorim.
Amorim zai fafata da Kocin Everton Moyes a ranar Asabar yayin da yake kokarin fitar da United daga koma bayan da ta ke fuskanta, tsohon kocin na Sporting Lisbon ya lashe wasanni huɗu ya yi rashin nasara a wasanni takwas a wasannin gasar Firimiya 12 da ya jagoranci Manche’ster United tun bayan zuwanshi a watan Nuwamba.
- Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu
- Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu
Moyes, wanda United ta sallama a shekarar 2014 bayan ƙasa da shekara guda yana jan ragamar horar da ‘yan wasan, tuni ya samu adadin nasarorin da Amorim ya samu tun bayan zuwanshi Old Trafford duk da cewa wasanni shida kacal ya jagoranta tun bayan komawarsa Everton a watan Janairu.
Everton, a matsayi na 14, tana sama da United wadda ta ke matsayi na 15 a teburin Firimiya gabanin haduwar kungiyoyin na karshe a Goodison Park,Everton wadda akewa lakabi da Toffees za su koma wani sabon filin wasa a kakar wasa mai zuwa.