Kungiyar dillalan tumatir ta yi barazanar shiga yajin aikin kai kayan tumatir zuwa Jihar Legas.
Dillalan sun dauki matakin ne saboda irin barnar da aka yi masu a kasuwar hada-hadar tumatir ta Oke-Odo a jihar.
- Bullar Annobar Cutar Kyanda Ta Tilasta Rufe Makarantu A Adamawa
- Xi Jinping Ya Kama Hanyar Zuwa Faransa Da Serbia Da Hungary Domin Ziyarar Aiki
Shugaban kungiyar dillalan, Alhaji Ahmed Alaramma ne, ya bayyana hakan, yayin da ya gudanar da jawabi ga manema labarai a Jihar Kaduna.
Shugaban ya kara da cewa mambobin kungiyar sama da 70 ne suka bayar da hayar kwanduna ga dillalan tumatir da aka lalata 60,000.
Ya kuma kara da cewa ana amfani da kwandon na roba ne saboda sassauta matsalolin asara.
Don haka shugaban ya ci gaba da cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun yi maganin faruwar irin hakan a gaba.