Dillalan Da Suka Shigo Da Albarusai 10,000 Cikin Nijeriya Sun Shiga Hannu

Rundunar ‘yan sandar Jihar Oyo, ta samu nasarar cafke mutum hudu wadanda ake kyautata zaton dilolin makamai ne, wadanda suke samar wa ‘yan fashi da makami bindigogi da kuma albarusai, domin su yi wa mazauna garin Ibadan babbar birnin jihar fashi.

Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Sina Olukolu, shi ne ya gurfanar da wadanda ake zargin ranar Alhamis a shalkwatar ‘yan sanda da ke yankin Eleyele cikin garin Ibadan. Ya bayyana cewa, an dai samu nasarar cafke su ne da albarusai masu rai har guda 10,000.

Mista Olukolu, ya kara da cewa, an samu nasarar damke wadanda ake zargi ne, bayan da rundunar ‘yan sanda sashen masu yaki da ‘yan fashi da makami da ke garin Ibadan, suka samu bayanai sirri game da maboyen ‘yan fashin da ke yankin Oke Bola cikin garin Ibadan.

Ya ce, wadanda ake zargin sun dade su na addabar mazauna yankin garin Ibadan da kuma wasu sassaan wasu jihohin kasar nan. “Bayan samun bayanai, nan take tawagar ‘yan sanda suka dauki mataki, inda suka samu nasarar ram da mutum hudu wadanda ake zargi kamar haka, Adekunle Abimbola, Abel Kojo, Mukaila Ariyo da kuma Ade Adebayo, a maboyensu da ke cikin garin Ibadan.

“An dai kwato albarusai masu rai har guda 10,000, karamar motar bas kirar Toyota Sienna mara lamba da kuma wata mota kirar Toyata Camry, mai lamba kamar haka GGE 979 FT, daga hannun wadanda ake zargi.”

Kwamishinan ‘yan sanda ya ce, rundunarsa za ta ci gaba da samar da wasu dabaru wadanda za su taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci a cikin Jihar Oyo. Ya bukaci mazauna jihar da su guji aikata ayyukan ta’addanci musammam ma lokacin bukukuwar babbar sallah. “Ya kamata mutane su dunga kiyaye wurin da suke zuwa, sannan kuma su kaurace wa ayyukan ta’addanci, domin su sani cewa, an girke jami’an tsoro a jihar wadanda za su kiyaye rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu,” in ji kwamishinar ‘yan sanda.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Abel Kojo, ya bayyana wa manema labarai cewa, bai da lasisin mallakar makamai, amma yana sayar wa mafarauta ne bindigogin. “Na kai kusan shekara ina gudanar da wannan sana’ar na sayar wa mafarauta bindigogi. Bana sayar wa batattun mutane bingigogi, domin su yi ta’addanci .”

Wakazalika, ‘yan sanda sun kara damke mutum uku wadanda ake zargin kasurguman ‘yan fashi da makami ne, wadanda suka kware wajen sayar da motocin sata. “Sun farmaki wani mutum mai suna Ayodeji Joshua a yankin Eleyele da ke cikin garin Ibadan, inda suka nuna masa bindiga, sannan suka kwace masa motarsa kirar Nissan Armanda Jeep da kuma wasu kayayyakinsa. Mutum biyu daga cikin maharan sun tursasa wa mutumin shiga bayan motar, inda suka yadda shi a kan hanya, yayin da na ukun daga cikin maharan ya tuka babursu kirar Bajaj, wanda suke amfani da shi wajen yin fashi da makami.”

“Lokacin da ‘yan sanda suka samu rahoton lamarin, tawagar ‘yan sanda sun samu nasarar samun ‘yan fashin a kan hanyar Ring da ke Ibadan, inda suke amfani da motar da kuma wata motar kirar Toyota Camry, wajen farmakin mutane tare da kwace musu dokiyoyinsu lokacin da suka nuna musu bindiga.” “Yan fashin sun ijiye motar, inda suka yi awon gaba da motar kirar Toyota. Amma ‘yan sanda sun ci gaba da farautar su. Daga baya dai ‘yan fashin sun yi mummunar hatsari a yankin Agodi da ke cikin garin Ibadan, sakamakon bin da ‘yan sanda suke musu. “Daga baya dai an samu nasarar cafke daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Folorunsho Adekunle, yayin da sauran suka gudu. An samu nasarar kwato dukkan motocin guda biyu da bindiga kirar gida tare da sunkin albarusai guda uku da kuma tsabar kudi har na naira 11,000, daga hannun wadanda ake zargin,” in ji ‘yan sanda.

Exit mobile version