Manoman inabi na samun riba mai yawa a Nijeriya, musamman idan manomi ya mayar da hankali wajen nomansa da yawa, da kuma sanin bukatar da ake da ita da iya kayyade farashinsa.
Idan manomi ya noma shi, a kadada daya, tsadar nomansa zai iya kai wa kimanin dala 1,500 zuwa dala 2,0000 a shekara, inda manomin zai iya samun ribar daga dala 2,500 zuwa dala 5,000 a duk shekara, kuma ribar da manomi ya samu a shekara, ta danganta ne da yawan amfanin da ya samu da kuma farashin.
‘Ya’ya Nawa Bishiyar Inibi Ke Yi ?
Duk da cewa akwai kalubale wajen nomansa da suka hada da sace wa wajen nomansa, da yawan jarin da ake zuba wa, sai dai za a dade ana cin moriyarsa, wanda a tushe daya na inda ana iya samun ‘ya’ya masu yawa a shekara, musamman idan an ba shi kulawar da ta dace. Bishiyarsa na iya kai wa shekara arba’in ana amfana da ita.
Lokacin Gyaran Gona:
Matakin farko na noman inibi shi ne, fara yin sharar gona da kuma noma shi a kasar noman da ta dace, za ka iya noma shi a kan nau’ukan kasar noma biyu da ake da su.
Lokacin Shuka Shi :
Hanya ma fi sauki wajen shuka shi, ka haka reni, shi ka saro jikinsa, kana iya yi masa aure, haka renonsa zai iya kai wa daga shekara uku zuwa shekara hudu kafin ya nuna, ana shuka shi daga watan Satumba zuwa watan Okutuba, inda kuma wanda aka saro jikinsa, za a iya dasa shi daga watan Fabirairu zuwa watan Maris, za ka iya shuka irinsa kamar 5,000 a kadada, inda ake bukatar ramin da za ka shuka ya ya dan yi zurfi fadinsa kuma ya kai kafa 12.
Lokacin Yi Masa Ban-ruwa:
Bai cika bukatar ban-ruwa ba, domin yana jure wa kowane irin yanayi, sai dai, idan ruwan sama ya ragu, kasa da mili mita 500 a shekara, dole ne ka yi masa ban-ruwa, domin inibi, na bukatar ruwan sama da ya kai yawan mili mita 900 kafin ya girma.
Kwari Da Cututtukan Da SuKe harbinsa:
Wasu daga cikin kwari da cututtukan da ke harbin inibi sun hada da wadda ake kira a Ingilishi da, bacteria wanda masana suka bayar da shawara a yi amfani da gaurayen maganin Bordeaud da ruwan ganyen darbejiya da ruwa da kuma kashin shanu.
Takin Zamani Da Ya Fi Dace Wa A Zuba:
An fi son manoninsa ya yi amfani da takin gargajiya wajen nomansa haka kuma ana son manominsa ka da ya zuba masa takin a shekarar farko da ya shuka shi, sai bayan shekara ta biyu, inda kuma a shekara ta uku, manomi zai iya yin amfani da takin da ya kai daga kilo giram 50 zuwa 60 a kadada daya
Lokacin Fara Dibansa:
Bai da wani takamaiman lokacin da aka kayyade za a iya dibansa, sai dai da zarar ya nuna za a iya dibansa.
Akasari an fi yin noman inibi a wasu kasashen da ke fadin duniya, sai dai, Nijeriya ba ta rungumi nomansa ba sosai kamar irin wadannan kasashen ba.
Bishiyoyinsa na da kyau, wadanda kuma ke samar da dandano da sauran nau’ukan na inibin, da ake sha a Nijeriya ana shigo da su ne daga Afirika ta Kudu, inda a yayin da aka shigo da shi cikin kasar, zakinsa ke ragu wa.
Ana sarrafa shi zuwa nau’uka daban-daban, kammar su kayan zaki da lemon Kwalba da man shafawa da sauransu, haka yana da sinadarin Minerals da bitamins da ke kara wa dan’adam karfun jiki.
Har ila yau, bishiyarsa na samar da kilo giram 25 na inibi, musamman idan an yi noman bisa fasahar noma ta zamani, nomansa ya fito ne daga Gabashin Asiya da wasu kasashen da ke a nahiyar Turai.
Kasar Sin da Faransa da Amurka da Safaniya da Fotugal da Argentina da kuma Afirika ta Kudu ne manya kasashen da ke kan gaba a fadin duniya wajen nomansa.
Inibi na shafe shekaru yana rayuwa, saboda haka ana bukata ka samo ingantaccen iri, don samun amfani mai yawa.
Sai dai, har yanzu a Nijeriya ba a rungumi wannan noma ba. Saboda haka akwai bukatar manoma su fahimci dimbin amfanin da ake samu daga noman na inabi.