Shugaban rundunar tsaro ta kasa, Janaral Lucky Irabor ya bayyana cewa dimokuradiyya ta zauna daram da kafarta a Nijeriya babau batun juyin mulki.
Ya ce rundunar sojojin Nijeriya za ta yi aiki kafada da kafada da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro na kasa wajen tabbatar da an gudanar da zaben 2023 a cikin kwanciyar hankali da lumana.
- Gina Al‘ummar Sin Da Afirka Mai Koshin Lafiya Ba Batu Ne Na Fatar Baki Ba
- Kuskuren Shugabannin Baya Ne Ya Jefa Nijeriya Cikin Tsaka Mai Wuya – Kwankwaso
Shugaban rundunar tsaron ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da jaruman sojojin da suka mutu a lokacin yaki na 2023, wanda ya gudana a Abuja.
Irabor ya ce, “Za mu tabbatar da cewa rundunar sojojin Nijeriya ta hada kai da ‘yansanda domin bayar da cikakken goyon baya wajen gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.”
Da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da shirye-shiryen sojoji kan zaben 2023, ya ce duk da jami’an ‘yansanda ne sahun gaba a lokacin zabe, sojoji za su mara musu baya domin ganin an gudanar da zabe lami lafiya.
“Na tabbar da cewa kun san ‘yansanda ne suke kan gaba wurin bayar da tsaro lokacin zabe. Na tattauna da babban sufetan ‘yansanda kan irin gudummuwar da za mu iya bayarwa wajen tallafa wa ‘yansanda lokacin zabe.
“Ina mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa rundunar sojojin Nijeriya za ta yi aiki kafada da kafada da ‘yansanda domin bayar da duk wata gudummuwa da ‘yansanda ke bukata.”
Ya kuma tabbata wa ‘yan Nijeriya cewa dimokuradiyya a kasar nan ba ta wata samun barazana daga juyin mulkin sojoji kamar yadda aka samu a wasu kasashen Afirka.
“Dimokuradiyya ta zauna daram da kafarta. Ta kasance gwamnati ta mutane, kuma ta jama’ar Nijeriya wacce ta zauna daram da kafafunta,” in ji shi.
Har ila yau, Irabor ya siffanta wannan bikin tunawa da gwarazan sojoji a matsayin sadaukarwa ga wadanda suke ganin su mutu domin kasarsu.
Ya ce “Bikin ba ranar tunawa da mamatan ba ne, ya kasance ranar da za mu nuna godiyarmu ga Allah mazanmu da matanmu wajen yin hidima ga kasarmu, kuma za mu ci gaba da hidinta wa kasar nan.
“Muna daukar irin wannan mataki wajen nuna soyayya ga kasarmu mazanmu da matanmu, wanda hakan ne ma ya sa akwai bukatar sadaukar da kai domin sauran mu su rayu. Ina ganin wannan shi ne ya fi cancanta.”
Tun da farko, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nazari kan bikin na karshe a matsayinsa na shugaban askarawan Nijeriya, a daidai lokacin da zai cika shekara takwas a kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Ya jagoranci manyan jami’an gwamnati a wajen kaddamar da bikin karshe na tunawa da gwarazon sojoji na wannan shekara.