Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya yi kira ga jama’a da su guji zuwa taruka da ba dole ba domin kare kansu da sauran jama’a daga kamuwa da cutar diphtheria.
Dakta Labaran ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba.
- Shirin Tsige Fubara: Gwamnonin PDP Za Su Gana Da Wike A Abuja
- Hatsarin Kwale-Kwale: Har Yanzu Ana Neman Mutane Sama Da 70 A Taraba – NEMA
A cewarsa, ya zama wajibi wajen wayar da kan jama’a kan wajibcin daukar matakan kariya da nufin dakile yaduwar cutar diphtheria a jihar Kano.
Kwamishinan ya ce cutar diphtheria cuta ce da ke yaduwa ta iska, don haka duk mutumin da ake zargin ya kamu da cutar ko kuma yake dauke da alamun cutar da su ziyarci likita don duba su.
Ya jaddada cewa a guji cudanya ta hanyar musabaha ko atishawa da mutane masu dauke da alamun cutar, inda ya bayyana cewa wadannan su ne manyan hanyoyin yada cutar.
Dakta Labaran ya ba da shawarar cewa idan yaro ne ya kamu da cutar, kada iyaye su bari ya je makaranta su gaggauta kai shi asibiti don yi masa gwaje-gwaje da duba lafiyarsa.
Kwamishinan ya gargadi mutane da su daina hada taruka marasa amfani musamman ganin yadda lokacin sanyi ke karatowa, lamarin da ka iya ta’azzara cutar diphtheria.
Ya kara da cewa idan taro ya zama wajibi, to ya kamata a yi a waje mai ishasshiyar iska.
Dokta Labaran ya bayyana cewa, babbar hanyar kariya daga cutar diphtheria ita ce allurar rigakafi, ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar da an yi wa ‘ya’yansu masu shekaru hudu zuwa 14 rigakafin sau uku a jere, domin kare su daga kamuwa daga cutar.
Har wa yau ya bayyana cewa idan yaro ya kamu da cutar amai da gudawa, dole ne a yi wa dukkan ‘yan uwansa allurar rigakafi don kare shi daga diphtheria da kuma wasu cututtuka.