Rahotanni daga birnin Lagos na cewa wani dan sanda da ke gadin bankin Sterling a unguwar Apapa, ya harbi wani direban motar haya kirar (Tanker).
A cewar rahoton nan take dai wanda aka harba din ya mutu.
Rahoton ya kara da cewa, hakan ya sa mutanen da ke wajen musamman sauran direbobi suka fusata suka yi kan ‘yan sandan da ke gadin bankin, inda su kuma suka ruga cikin bankin don neman mafaka.
Hakan ya sa sauran direbobin suka cinnawa bankin wuta.