Khalid Idris Doya" />

Dogarin Shugaban Kasar Faransa Ya Rasa Aiki Kan Cin Zarafi

Matakin sallamar shugaban masu kula da lafiyar shugaban kasar Faransa ya biyo bayan fitowar bidiyo da ya nuna yana dukan mutane a wurin zanga-zanga a ranar daya ga watan Mayu.

Jaridar Le Monde da ta wallafa bidiyon ta ce an gano dogarin Aledandre Benalla yana jan wata mata a wurin zanga-zanga, daga bisani aka ganshi yana dukan wani mutum. ofishin shugaban kasar ya dau matakin dakatar da shi na tsawon kwanaki 15 bayan faruwar lamarin a cikin watan Mayu.

Sai dai ‘yan daawa sun yi ca kan batun gami da tabka zazzafar muhawara a majalisa, kan rashin daukar tsauraran matakan gaggawa bayan faruwar lamarin.

A na cigaba da tsare dogarin shugaban tare da amsa tambayoyi, yayin da masu sharhi ke ganin batun ka iya shafar tasirin siyasar shugaba Macron.

Exit mobile version