Manyan jami’an Philippines sun sake ikirarin shirin sayen makamai masu linzami dake cin matsakaicin zango na Amurka tare da hada su da batun tekun kudancin Sin. Hakika matakin na Philippines ya damka muradun kasar na tsaro a hannun kawayenta na yammacin duniya.
Dabarar Philippines ta dogaro da kasashen yamma ba za ta samar da tsaro a kasar ba, sai ma akasin hakan. Saboda jibge makamai masu linzamin ya shafi tsarin tsaro na kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN.
A daya bangaren, Philippines na yunkurin cin gajiyar tekun kudancin Sin ta hanyar samun goyon baya daga kasashen dake wajen yankin, inda take ci gaba da takala da tada rikici da ma amfani da batun a matsayin wata dama ta jibge makamai masu linzami na Amurka, wanda yake tura yankin tekun kudancin Sin cikin hadari. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp