Aisha Seyoji" />

Dogon: Kabilar Da Ta Ce Ta Samo Asali Daga Tauraron Sama

A can kasar Mali, kudancin Afrika akwai wata kabilar da ke rayuwa da ake yiwa lakabi da suna Dogon. A yau mun kewaya duniya inda mukaci karo da mutanen kabilar Dogon, filin namu na yau zai sadaku ne da su.

Hasashe ya nuna cewa su dai wadannan mutane ‘yan asalin kasar Masar ne (Egypt), sannan tarihi ya nuna cewa sun kasance a wajejen tun shekarar 3200 kafin haihuwar Annabi Isah (B.c).

A yanda al’adansu ya nuna, tauraron sirius ya kasance yana da dan’uwa wanda ya kasance boyayye (inbisible) ga bil’adama. Shi dai wannan dan’uwa ya kasance mai matukar nauyi yana kuma kewaya tauraruwar ta Sirius. Tarihi ya nuna cewa wasu Al’umma daga sirius masu suna Mommos sun kawo ziyara cikin duniyar bil’adama dubbannin shekaru da suka shude. Su dai Mommos sun kasance munanan gaske ne, masu wata irin halitta da ta yi kama da ta ‘yan ruwa. Sun sauko a duniyar bil’adama a cikin  wani abu mai kama da halittar tsuntsu wanda ya kasance ya fidda kara mai matukar sauti, a yayin da ya sauka ya taba kasa. Sannan kuma ga iska mai karfi. Toh wadannan Mommos su ne wadanda suka baiwa mutanen dogon ilimi a kan tauraro sirius B. Sannan kuma suka kara da basu wadansu dadadan labarai a kan tamu duniyar, suka ce mus u Tauraruwar ‘Jupiter’ tana da wata guda hudu, suka kara da cewa satun tana da zobba.

Tattalin Arziki

Sana’ar noma itace ta kasance jagaba kima mafi rinjaye ga al’ummar Dogon inda suke noma, hatsi, dawa, shinkafa, albasa, wake, ganyen taba da duk suna nomawa. Sauran sun hada da ridi, masara, gyada, doya, dankalin hausa, tumatur, barkono, kubewa, kankana, abarba da Auduga. Kabilar dogo sukan shuka sannan kuma su kula da bishiyoyi kamar su dabino,idan kuwa aka dangantasu da makotansu fulani,kiwo yakasance abu marar muhimmanci, akan ajiye dabbobine kawai domin nuna matsayin arziki da kwarjini akasin ajiyeau domin kudi ,muhimman dabbobi sun hada da, raguna, awaki, jakuna, karnuka, kaji, zakaru, agwagi ‘yan tsirarun shanaye, dawakai da kuliyoyi kadan daga cikin wasu kauyukan kuma sukan kiwata zuma.

Rabe raben ayyuka

Akan raba ayyuka ne ta hanyar banbance tsakanin jinsi,kere kere da gine gine.maza sukan kula da dabbobi, suje farauta sannan su gyara gona yayinda mata ke da alhakin dinki, nome ciyayi da kuma girbe amfanin gona, yayin da kuma suke shuka wasu ababuwan amfani kamarsu Albasa. Mata da maza suna saye da sayarwa, su (kamun kifi) da kuma tara abinci irin na daji.

Auratayya

Namiji yana da damar ya auri mace daya jallin jal, duk da dai a wasu lokutan a kan iya dagawa namiji kafa ya auri mace fiye da daya amma fa ba zai taba auren mace fiye da biyu ba a dokance.

Iyaye ne suke zaba wa ‘ya’yayensu abokan zama na farko, masu aure na biyu su ne suke da damar zaban abokan zama. Aure yakan kasance tsakanin mutanen da suka fito tsakanin kabila daya ko kuma ‘yan’uwa daga wasu kabilar. Haramunne kulla alakar auratayya da mutumin da yake sana’ar kira (blacksmith). Bayan mace ta haifi danta na farko zata kasance ne a gidan iyayenta yayin da mijinta zai koma zama a gidajen marasa aure inda ya yi zaman kuruciyarsa daga shekaru takwas zuwa goma(8-10). Akan yi saki, sannan a lokacin da saki ya gifta har ya kasance cewa mace za ta koma gidan iyayenta, to fa za ta tafi ne kawai da mafi kankanta a cikin yaranta, sauran kuwa su zauna da mahaifinsu.

Zamantakewa

A zamanin da can baya, mutanen Dogon sun kasance mafadata, sukan yi tashin hankali tsakaninsu da sauran makotansu kabilu kamar fulani, har sai da zamantakewa da auratayya ta hada su da sauran kabilu kamar kabilar Bozo tukuna sannan abubuwan suka yi sauki.

Addini

Mafi girma a jerin ababen bauta shi ne Amma, Amma ya kasance mafi girman abin bauta, a cewarsu shi ne mai rayawa da kashewa, mai ganin kowa da komai ya kuma san komai. Shi ne ya halicci wasu abababen guda uku, kamar su Mommo, yaron Amma wanda ake dangantashi da dan ruwa, Lebe wanda alhakin duniya da ababen cikinta ke wuyansa, da kuma Yurugu mai wakiltar mutum.

Duk da cewar muatanen Dogon sun yi imani da Amma a matsayin mafi girman abin bauta inda har akwai addu’o’i da hadaya gareshi , sun yi imani kuma dai da wadansu Allolin na daban, ta hanyar kungiyar asiri ta masks, kungiyar asiri ta lebe da binu. Yaduwar addinin Musulunci a Afrika ya kawo canje canje ga mutanen Dogon. Inda wasu suka karbi addinin muaulunci, wasu kuma suka ki ko yi da shi. Makotansu fulani sun taka rawar gani wajen karfafawa wa mutanen Dogon guiwa wajen karbar addinin Islama, kashi goma bisa dari na kabilar Dogon sun kasance mabiya addinin Kirista.

Bukukuwa

Muhimman bukukuwa ga wadannan al’umma sun kasance bikin noma da kuma bikin mutuwa, bikin shuka (bulu) yana farawa watan Afrilu da Mayu, daf da fara saukar ruwan sama, a dukkan kauyukan yankin  a lokacin kannan biki akan ba da hadayar hatsi daga gonar dogon tare da hadaya daga bintu priest (binukedine) domin tabbatar da damina da girbi mai albarka.

Bikin bisne mamaci a Al’adar dogon ya kasu kashi biyu: bikin farko wanda ake yin sa nan da nan bayan mutuwar mamaci wanda kuma zai ci gaba da kasancewa har sati daya da yin mutuwar, sai kuma dama wanda ake fadada biki wanda kuma shi ne yake alamta cewa lokaci na bakin ciki ya kare, lokacin bikin akan yi hadaya ta dabbobi, kade-kade da raye-raye, akan banbance bikin mutuwa ne ta hanyar shekaru da kuma matsayin shi mamaci.

Bison mata ya kasance mai sauki da kuma takaitaccen biki, a daya a kowacce shekara sittin na rayuwar kabilar Dogon, Sigi (sigue) biki mai muhimmanci yakan kasance. Ada can baya akan yi bikin ne domin karrama matattun ababen bauta, wanda yanzu kuma ya zama ake yi wa wadanda suke raye, ana yin wannan bikin ne domin kankare ko share zunuban da kuma munanan tunani na mutanen gari .Kadekade da raye-raye kan dau dumi tsakanin mutanen domin kayatar da makotansu wanda ya hada da ciye- ciye, shaye-shaye, sannan kuma a nuna bajinta wajen dukiya.

Mutuwa da rayuwa

Sukan dauki mutuwa a matsayin wani abu da ke raba tsakanin jiki biyu. Nyama (rayuwa), kikinu (ruhi) su ne ake danganta su da mutuwa, dama shi ne bikn da ake yi wa mamaci. A cewarsu kurwar mamaci yana yawo ne a cikin kauyen jeji, ko kuma gidan da yake zaune kafin ya mutu har sai lokacin da aka gama bikin dama, bayan an gama bikin sai kuma kurwar mamacin ya bar duniyar mutane inda zai koma wajen Allansu ‘Amma’.

Exit mobile version