Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gargaɗi al’umma cewa duk wanda ya ƙi taimakawa jami’in ‘yansanda a lokacin da yake buƙatar taimako, zai iya fuskantar hukuncin tara ko ɗauri.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce sashe na 99 na dokar ‘yansanda ta 2000 ya bayyana cewa wanda ya ƙi taimaka wa jami’in ‘yansanda da ke cikin hatsari ko fuskantar turjiya, zai iya fuskantar hukunci.
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
- Sin Na Bukatar Ma’aikatan Masana’antu Masu Kaifin Basira Fiye Da Miliyan 31 Zuwa 2035
“Duk wanda aka kira ya taimaka wa ɗan sanda da ke cikin hatsari, amma ya ƙi ko ya yi watsi da buƙatar, ya aikata laifi da zai iya janyo tarar Naira 100,000, ɗaurin wata uku, ko kuma duka biyun,” in ji sanarwar.
‘Yansandan Nijeriya na da alhakin tabbatar da tsaro da doka a cikin ƙasa, amma sau da yawa ana samun ƙorafe-ƙorafe kan yadda suke gudanar da aikinsu.
A shekarar 2020, an gudanar da gagarumar zanga-zanga a ƙasar, wadda matasa suka jagoranta don yin adawa da cin zarafi da ake zargin wani ɓangaren rundunar mai suna SARS da aikatawa.
Wannan zanga-zangar ce ta sa aka rushe ɓangaren.