• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dokar Hana Aikin Tilas Ko Dokar Neman Durkusar Da Tattalin Arzikin Sin?

by CMG Hausa
3 years ago
xinjiang

Amurka ta fara amfani da dokar da ta zartar dake ikirarin hana aikin tilas a jihar Xinjiang ta kasar Sin a jiya.

Dokar na nufin kin karbar kayayyakin da aka samar a jihar, har sai an gabatar da shaidun dake tabbatar da cewa, ba ta hanyar aikin tilas aka samar da su ba.

  • Sin Tana Adawa Da Dokar Hana Kayayyakin Da Suka Shafi Jihar Xinjiang Shiga Amurka

Rahotanni sun nuna cewa, Xinjiang ce ke samar da kaso 20 na audugar da ake amfani da ita a duniya. Kuma a lokacin girbin auduga, ba al’ummar jihar kadai ba, har wasu daga sauran sassan kasar Sin na zuwa Xinjiang domin gudanar da aiki don samun karin kudin shiga. Shin idan har da gaske aikin tilas suke yi, me ya sa wasu za su niki gari su tafi inda ake aikin tilas? Wannan ikirari na Amurka na tattare da ayoyin tambaya.

Sanin kowa ne cewa, rashin aikin yi, shi ne tushen rikici a yankuna daban daban. A ganina, ban da saurin ci gaban tattalin arzikin Sin mai juriya da ya tsonewa Amurka ido, akwai ma zaman lafiya da kasar ke morewa da kuma ammana da gwamnati da al’ummarta suka yi, wanda ya yi hannun riga da yanayin Amurka.

Kullum Amurka da kawayenta na yayata batun kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, amma abubuwan da take yi ba sa dacewa da furucinta. Wannan doka a ganina, wani yunkuri ne na dankwafe ci gaban tattalin arzikin Sin da ma musgunawa al’ummar Xinjiang da take ikirarin karewa. Tun da noman auduga jigo ne a jihar Xinjiang, me zai faru idan aka daina sayen audugar a duniya? Wannan ba shi ne keta hakkin bil adama ba? Wato toshe musu hanyar samun kudin shiga, da zai shafi walwalarsu da yanayin zaman takewa.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Kamata ya yi Amurka ta zartar da dokokin da za su amfani al’ummarta kamar na hana mallakar bindiga da yaki da annobar COVId-19 da tunkarar matsalar tashin farashin kayayyaki, ba zartar da dokokin kan kayayyakin Sin ba.

Wannan mataki na Amurka, ba kamfanonin Xinjiang za su shafa kadai ba, har da kamfanonin Amurkar. Idan Amurka ba ta duba halin da za ta jefa ma’aikata da kamfanonin Sin ba, ai ya kamata ta duba na al’ummarta idan har ta damu da su.

An riga an shaida cewa, tubalin karfin tattalin arzikin kasar Sin ne samun gagarumar gudunmawa daga kasuwar cikin gida saboda yawan al’ummarta. Kana ba Amurka ce kadai ke cinikayya da Sin ba, don haka, matakin ita da al’ummarta zai fi yi wa tasiri ba kasar Sin. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
‘Yan Majalisar APC Takwas Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Kebbi

Adamu Yana Ganawar Sirri Da Sanatocin Da Za Su Yi Wa Jam'iyyar APC Takara

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.