Masu madafun iko, sun yaba da kudirin dokar masana’antar man fetur (PIB), a matsayin maganin matsalolin da ake fama da su a bangare man fetur a Nijeriya. A cewarsu, wata doka ce mai muhimmanci da ta yi alkawarin tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma rarraba arzikin man fetur na kasa, yayin da kurar take lafawa, gaskiya ta bayyana cewa; ba za a cika alkawuran ba.
Gudanar Da Kamfanin NNPC A Kan Tafarkin Mafarauta
Bisa ga sabbin bayanai daga Hukumar Kula da Makamashi ta Amurka, Nijeriya na cikin jerin matsayi na 11 a duniya; kuma ta hudu a Afirka wajen hako danyen mai a watan Satumbar 2023, da ganga miliyan 1.14 a kowace rana. Yayin da adadin yawan danyen man da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur(OPEC) ta amince da shi a watan Disamban 2023, ya kai kimanin ganga miliyan 1.72 a kowace rana.
- Sin Da Angola Sun Daga Matsayin Dangantakarsu
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
Har ila yau, matatun mai hudu mallakar gwamnati a Nijeriya da aka gina a tsakanin 1965 zuwa 1989, duk suna rufe ne na tsawon shekaru barkatai, sakamakon rashin tattali da kulawa. Jimullarsu a rana na iya tace ganga 445,000. Haka kuma, a cikin watan Disambar 2023, bayanan da aka samo daga Kamfanin KNOEMA, wanda yake dandamalin samun bayanai ne na duniya, yana nuni da cewa; ganga 520,000 ake bukata a kowace rana a Nijeriya.
Kazalika, bayanai sun nuna a shekarar 2019, gwamnati ta bayar da lasisi kusan 43, domin gina manyan matatun mai na zamani da kuma matsakaita, wanda a cikinsu kusan matatun mai guda hudu ne kawai ake tsammanin suke aiki tare da ba da jimullar ganga 34,000 a rana.
Matatar Dangote da za ta ci dala biliyan 19, wanda aka kaddamar da ita a shekar 2023, amma har yanzu ba ta fara aiki ba, tana iya samar da ganga 650,000 a kowace rana. A maimakon NNPC ta yi amfani da Asusun Albarkatun ‘Sobereign Wealth Fund (SWF)’, ta sayi hannun jari a matatar mai na Dangote, sai ta kirkiro wani salo wai shi ‘Project Bison’ ta yi gaban kanta wajen sayen da kuma samun hannun jarin kashi 20 cikin 100 na matatar man a kan dala biliyan 2.76.
Wani abun al’ajabi kuma abun takaici shi ne, za ta dinga bayar da ganga 300,000 a kowace rana na danyen man ga matatar man Dangote a cikin rangwame tare da rasa ribar da za a bayar na kashi 100 cikin 100 a lokacin da ta ke biyan bashin sayen hannun jarin matatar man na Dangote.
Bugu da kari, ta ‘Project Gazelle’, an karbo rancen dala biliyan 3.2 daga bankin AFREDIM, domin tallafa wa rikicin Dalar Amurka da Nijeriya ta samu kanta a ciki ,yayin da za a biya bashin ne ta hanyar bayar da danyen man.
Haka zalika, idan aka yi la’akari da cewa, kamfanin na NNPC ya mallaki gangar mai 130,000 a kowace rana daga Dangote, hakan na nufin cewa, kamfanin NNPC na iya gina sabuwar matatar mai a kan wannan adadi, amma duk da haka ta ci gaba da kulla yarjejeniyar gyara matatar mai na Fatakwal, wadda tsohuwar matatar mai ce, da ba a iya samun kayan gyaranta a cikin kasuwanin duniya, a kan dala biliyan 1.5 a cikin shekarar 2021 tare da cewa, za a kammala gyaran mataki na biyu a cikin watanni 44 (wato Yulin 2024). Ba a san matsayin gyaran mataki na daya ba, yayin da babu tabbas kan matsayin sauran matatun man guda uku.
Shin Mallakin Waye Man Nijeriya?
Ya kamata Nijeriya ta yi amfani da arzikin man da Allah ya ba ta ne, ta wajen yin ayyuka daban-daban da suka hada da gudanar da kasafin kudin gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi, sai zuba jari a fannonin ababen more rayuwa kamar, ilimi, kiwon lafiya, noma da kuma yi wa al’umma masu zuwa nan gaba tanadin da ya dace. Amma Kash, sai dai kuma ana fama da matsalar rashin da’a da cin hanci da rashawa da rashin amana, lamarin da ya haifar da rashin samun ci gaba da walwala a tsakanin al’umma baki-daya.
A cewar WIKIPEDIA, asusun ajiyar arziki na Nijeriya (SWF), wanda aka kirkiro saboda tanadi da kuma saka wasu daga cikin kudaden shiga na man fetur tare da daidaita tattalin arziki a lokacin karyewar farashin mai, wanda aka kafa a 2011 da jari na dala biliyan 1. Yanzu haka, yana da dala biliyan 2.3, wato karin dala biliyan 1.3 kacal aka samu a cikin shekaru 12. Abin tambaya a nan shi ne,shin nawa aka salwantar a kan albashi da ribar ofis a cikin wadannan shekaru 12?
Abin da ya sake daure kai shi ne, kamfanin NNPC ya aike da jimullar kudi dala biliyan 2.7 zuwa asusunta na babban bankin Nijeriya (CBN), daga watan Janairu zuwa Yunin 2022. Hakan ya kasance kafin a sanya hannu a kan PIB. Daga cikin dala biliyan 2.7, dala miliyan 645 na hannun jarin NLNG ne, yayin da dala biliyan 1.78 ta fito ne daga ayyukan kamfanin NNPC. An kasa samun ingantattun bayanai kan nawa ne kamfanin NNPC ya aika wa bankin CBN tun lokacin da aka sanya hannu a kan PIB. Ku tuna cewa, PIB an gaya mana cewa; niyyar kudirin shi ne gyara fannin mai da iskar gas da kuma samar da sabon tsarin kula da masana’antu da canza matsayin NNPC daga kamfanin gwamnati zuwa kamfani mai cin gashin kansa, wanda ake sa ran zai kara gudanar da ayyukansa yadda ya kamata kuma a bayyane.
Dalilai Marasa Kan Gado
An sanar da ‘yan Nijeriya cewa, tsohon tsarin na kamfanin NNPC na da illoli da yawa kamar haka:
i- Dogaro da kudaden gwamnati, inda hakan ya jawo karancin gasa da sha’awar masu zuba jari na duniya.
ii- Tasirin siyasa da tsaikon da ake samu na ofis, wanda ke sa kamfanonin mai na duniya rashin jin dadin yin kasuwanci da kamfanin NNPC.
iii- Kamfanin NNPC na da ma’aikatan da aka dauka aiki, domin dalilan siyasa, wanda ke kawo cikas ga nasararsa a matsayinsa na kamfanin kasuwanci. A halin da ake ciki yanzu, matatun mai guda hudu ba sa aiki kuma har yanzu ana biyan dimbin ma’aikatansu duk wani hakki ba tare da samar da digon mai ba.
ib- Kamfanin na NNPC na yawan siyar da mai bashi tare da tara yawan basussuka, wanda hakan ya kawo cikas ga ayyukansa. Amma ku tuna cewa, sun aro dala biliyan 3.2 daga bankin AFREDIM, wanda za a biya shi da danyen mai.
b- Kamfanin NNPC ya samu karancin kudaden shiga da kuma karancin ribar da yake samu, wanda hakan ya kawo cikas ga nasarar kamfanin. Amma kuma mu tuna kwanan nan shugaban kasa ya bayar da umurnin su rika tura kudi zuwa asusun bankin CBN.
Haihuwar Dokar PIB
Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021, mai lambar Gazette 142, wani kundi ne da ke da babi 5, sashi 319 da kuma jadawali 8. Daftarin ya kunshi abubuwa masu matukar razanarwa da firgitarwa da kuma tayar da hankali da za su yi tasiri ga rayuwar sama da ‘yan Nijeriya miliyan 200.
Kamar tsarin farashin mai a gida, tsarin farashin gas don amfanin masana’antu masu amfani da gas, rarraba kashi uku cikin 100 ga al’ummomin da ake samun albarkatun mai a kasashensu tare da bayar da kashi 30 cikin 100, domin ci gaba da nemowa da kuma hako man fetur (Frontier Basins) da sauran makamantansu. Bayar da ba’asi a kan wadannan abubuwa, ba zai samu ba sakamakon rashin sarari a wannan shafi.
Nakudar Haihuwar PIB:
1- Hukumar PIB, ta tanadi kafa sabbin kamfanoni irin su NNPC da ma’aikatar man fetur ta kasa da kasa da hukumomi biyu da al’ummomin da suka karbi bakuncinsu da kuma rusa ko canja wurin wasu kamfanoni kamar NNPC, Sashen Albarkatun Man Fetur da Asusun Daidaita Man Fetur. Har ila yau, da damar canja wurin bayar da lasisin man fetur da hanyar kwangiloli da yarjejeniyoyin kadarori da lamuni da ma’aikata zuwa sabbin kungiyoyi ko shirye-shirye a cikin kayyadaddun lokuta da yanayi. Aiwatar da wannan aiki zai fuskanci kalubale kamar takaddamar shari’a, tsoma baki na siyasa da dai sauransu.
2- PIB na bukatar habakawa tare da samar da fasaha na duniya da kuma hanyoyin samar da kudade na sabbin ma’aikatun da aka kirkiro. Tabbas wannan zai zama mafi kalubale sakamakon rashin kwarewa da kuma rashin kyawawan na’urorin fasaha da dai sauran makamantansu.
3- PIB na bukatar kafawa tare da aiwatarwa da sa ido da kimantawa da samar da hanyoyin gudanar da dokokin PIB da kuma tanade-tanadensa. Wannan zai yi wuya saboda rashin ingancin bayanan da za su wadatar da kuma cewa, wadanda suka rattaba hannu wajen kirkiro da dokar su ne ke jan akalar wannan sashe na albarkatun mai.
4- Da dai sauransu.
Wa Zai Aiwatar?
PIB ya zama wani abu da masu madafun iko ke amfani da shi, don ci gaba da yin sama-da-fadi da dukiyar kasa.
A wannan lokaci, ya zama wajibi ‘yan Nijeriya su tashi tsaye wajen yakar wannan zalunci da wargaza wannan fage na yaudara.
Shawara a nan ita ce, dakatar da amfani da wannan daftari na PIB tare kuma da komawa ga tsarin da ake kai a da kafin ya zama YASHIN da Nijeriya za ta nitse a cikinsa.