Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shigar da kara a gaban kotun koli inda suke kalubalantar ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas da shugaba Bola Tinubu ya yi.
A ranar 18 ga watan Maris ne shugaban kasar ya ayyana dokar ta-ɓaci, inda ya yi ikirarin sashe na 305(5) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 ne ya bashi hurumin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida, yayin da ya sanar da VA Ibok-Ete Ibas mai ritaya a matsayin wanda zai kula da jihar shi kadai.
- Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
- Ƴansandan Sun Gayyaci Sanata Karimi Kan Zargin Shigar Kungiyar Leƙen Asirin Rasha Majalisa’
Gwamnonin PDP da suka hada da shugabanni daga jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, da Zamfara, sun ce shugaban kasa ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna da mataimakinsa a dimokuradiyya, inda suka kara da cewa nada wani a matsayin mai kula da jihar ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
A cewar takardun kotun, gwamnonin suna neman a bayyana cewa, hukuncin da shugaban kasa ya zartar ya saɓa wa sashe na 1 (2), 5 (2), da 305 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Sun kuma kara da cewa, shugaban kasa ba shi da wani iko ko kadan na dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakin gwamnan wata jiha a tarayyar Nijeriya bisa fakewa da dokar ta-ɓaci.
Gwamnonin kuma suna kalubalantar amincewa da dokar ta-ɓaci da majalisar dokokin kasar ta yi, suna masu cewa, yin amfani da kuri’a jin ra’ayi ta baki ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar, saboda dokar ta ce, dole sai an samu mafi rinjayen kuri’a biyu cikin uku na dukkan ‘yan majalisar.
A cikin jawabin da suka gabatar wa kotun, masu shigar da kara sun kara da cewa, dokar ta-ɓacin ba ta cika ka’idojin tsarin mulki da sashi na 305 ya gindaya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp