Tun bayan lokacin da aka kamo Nnamdi Kanu daga Kasar Kenya, kungiyar IPOB ta gudanar da zanga-zanga daban-daban da daukar haramtattun matakai ciki har da aiwatar da dokar zama a gida a duk ranekun Litinin har sai an sako Nnamdi Kanu.
Masana da dama na ta tofa albarkacin bakinsu a kan tasirin da matakin ya yi musamman a yankin Kudu maso Gabas da ma kasa baki daya.
Har ila yau a bangaren Gwamnatin Tarayya, musamman yanzu da aka tabbatar da nadin sabbin manyan hafsoshin tsaro, an fara daukar mataki a kan ‘yan haramtacciyar kungiyar ta IPOB.
Sabon salon da IPOB ta zo da shi domin matsin lambar a saki shugabanta tun daga ranar 9 ga Agustan 2021 ta yi tsanani a yankin Kudu maso Gabas. Har ta kai ga rabuwar mazauna yankin da wasu ‘yan’uwansu. A halin yanzu Litinin ta zama wani bangare na karshen mako. Bankuna, shaguna, kamfanonin sufuri, coci-coci, makarantu da ofisoshin gwamnati dukkan su a kulle suke kasancewa.
Ranekun Litinin 82 da aka tafka asara a cikinsu
Wani masanin tattalin arziki, Dakta Dozie Okeke, ya shaida wa manema labarai cewa, ba za a iya kididdige mummunar tasirin da wannan doka ta zaman gida ta haifar ga tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas ba.
Ya ce: “Tun daga ranar 30 ga Yulin 2021, lokacin da kungiyar ta ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB) ta sanar da cewa za ta kafa dokar hana fita a duk ranar Litinin a yankin har sai an sako shugabanta, Kanu, al’ummar yankin Kudu maso Gabas ke cikin wannan hali na zaman gida fiye da Litinin 82 tun lokacin da dokar ta fara aiki a ranar 9 ga Agustan 2021.
“Ko shakka babu wannan doka ta zaman gida ta jawo wa mazauna yankin Kudu maso Gabas asarar rayuka da dukiyoyi. Tun daga lokacin da aka fara wasu ‘yan asalin yankin da ba su ji ba ba su gani ba sun rasa rayukansu ta hanya mafi muni, tare da hana iyalai ganin ‘yan uwansu wadanda a wasu lokuta su ke nemo musu abin da za su ci gami da yi musu tabo da ba zai taba warkewa ba a rayuwarsu.
“Daya daga cikin al’amuran da suka fi tayar da hankali shi ne kisan gillar da aka yi wa Dakta Chike Akunyili (mijin marigayiya Dora Akunyili), wanda harsashi ya fasa kansa da tsakar rana, kuma aka dauki hoto tare da nunawa ta yadda zai sanya damuwa ga dukkan dan kasa nagari.
Tun bayan wannan kisan, wasu da dama sun rasa rayukansu a hannun ‘yan bindiga da ke tilasta aiki da wannan umarnin na dokar zama a gida.”
Tasirin da lamarin ya yi a kan tattalin arziki
“Wannan zanga-zangar ta yi tasiri sosai ga tattalin arzikin Kudu-maso-Gabas, kuma, hakika, ta shafi tattalin arzikin Nijeriya. Wani bincike da cibiyar bincike ta kasa da kasa (ICIR) ta gudanar, ya nuna cewa kananan sana’o’in yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya sun yi asarar Naira tiriliyan 5.375, kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 12.215 a ranakun Litinin 82 tsakanin 9 ga Agustan 2021 zuwa 19 ga Disambar 2022.
An yi asarar Naira tiriliyan 5.375 daidai da (dala biliyan 12.215) a cikin wannan yanayi.
“Tsarin sufuri wani bangare ne mai muhimmanci a yankin domin yankin shi ne ke da mallakin babbar kasuwar Onitsha da kasuwar Aba; da ke bukatar kwararar mutane da yawa a yankin domin hada-hada. Sai dai wani rahoton da gidauniyar DebEast da SBM Intelligence ta fitar ya bayyana cewa masu safara suna asarar makudan kudaden da suka kai Naira biliyan 10 daidai da Fam miliyna (£18.5m) a duk ranar zaman gida.
Wannan dai wani lamari ne mai matukar ban takaici ga kasar da tuni tattalin arzikinta ya durkushe, domin rage kudin shiga na nufin rage karfin kasuwancin masu safara a yankin Kudu maso Gabas, tare da rage yawan harajin da ma’aikatan ke bai wa gwamnatocin jihohi.
“Masu zuwa cin kasuwa ko dillalan da ke yin odar kayayyakin ma abin ya shafe su saboda ba sa samun damar shiga da kayansu. Wannan ya sa suka rasa kwarin gwiwa wajen mu’amala da kayayyakin da manyan masu kawo kayayyaki daga Kudu maso Gabas suke yi.”
Hakazalika, LEADERSHIP Weekend ta ruwaito cewa, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu, ya ce an yi asarar kimanin Naira tiriliyan 4 sakamakon dokar zaman gida a yankin Kudu maso Gabas a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Kalu ya ce yanayin da ake shiga a kowace ranar Litinin a yankin a jihohi biyar da suka hada da Abia, Anambra, Enugu, Ebonyi da Imo ya gurgunta harkokin kasuwanci tare da dakile damar ci gaban tattalin arziki.
Mataimakin kakakin ya bayyana hakan ne cikin wani muhimmin jawabi da aka gabatar a taron ‘Bunkasa Kasuwanni na 2023’ mai taken: “Kaddamar da Hadin kai tare da ‘yan kasuwa ta hanyar tsarin kirkira, fasaha, tantancewa da dorewa” da aka gudanar a Legas.
Kalu ya ce wannan umarni ya tilasta wa masu son zuba hannun jari ficewa daga yankin Kudu maso Gabas, inda ya ce tashe-tashen hankula na da nasaba da yankin, ya kuma yi kira da a hada kai da ‘ya’yan kabilar Igbo maza da mata domin kawo karshen wannan matsala.
Ya ce: “Abubuwan da ke damun ‘yan kabilar Igbo a halin yanzu shi ne rashin tsaro da dokar zaman-gida a yankin Kudu-maso-Gabas. Sauye-sauyen wannan matsala ba a iya ganewa.
“A halin yanzu muna kallo a karo na biyu na irin wannan hijirar da ‘yan kabilar Igbo ke yi na kasuwanci, a wannan karon, saboda rashin tsaro da kuma matsalar zaman gida a yankinmu da muke so.”
Kalu ya kuma yi kira da a sake farfado da tsarin koyar da ‘yan kabilar Ibo, al’adar da aka jarraba a lokuta da dama, wanda a cewarsa hakan ya samar da ’yan kasuwa maza da mata da suka yi nasara, yana mai jaddada cewa bai kamata a bar tsarin ya ruguje ba.
Ya ce zai yi aiki da ’yan majalisar da suke wakiltar yankunan Kudu-maso-Gabas a Majalisar Dokoki ta kasa wajen lalubo bakin zaren warware matsalar da kuma kara himma a kan sake farfado da yankin.
Fannin Ilimi
A nasa ra’ayin, wani masani a fannin tattalin arziki da yake tare da kungiyar ‘‘Masana tattalin Arziki ta Nijeriya’, da wata kungiya mai zaman kanta mai suna Economic Think Tank, Olabisi Ayoola, ya koka da tasirin dokar a fannin ilimi.
Ya ce: “Shekaru da dama, yankin yana alfahari da kansa a fannin ilimi, inda dukkanin jihohi biyar dake cikin jihohi 10 aka ayyana su a matsayin wadanda suka fi kwazo a hukumar shirya jarabawar ta Yammacin Afirka da hukumar shirya jarabawar ta kasa, sannan a kalla jahohi biyu ne a jerin jihohi biyar din suka shiga sahun farko.
“Zaman gida a halin yanzu yana kawo cikas ga kalandar ilimi a duk matakan ilimi saboda ba za a kammala manhajoji daban-daban a lokacin da aka kebe ba.
“Akwai lokutan da ‘yan daba masu aiwatar da wannan doka suka fatattaki daliban da ke rubuta jarabawar da Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta gudanar. Sun kuma kona babura na malamai da na dalibai, tare da gargadin su da su bi umarnin wannan doka ta zama a gida.
“A koyaushe makarantu a kulle suke a duk ranekun Litinin. Babu wani abu da makarantar za ta iya yi a kai domin babu wasu iyaye da ke son jefa rayuwar ‘ya’yansu cikin hadari. Har ma yana da wahala a matsayinmu na malamai mu iya zuwa makarantu.
“Har ila yau, an bayar da rahoton koma-bayan jarrabawa masu matukar muhimmanci, wanda hakan ka iya yin barazana ga kimar yankin game da ingancin ilimi, wanda tuni wadannan alamu sun riga sun fara bayyana.
Dangane da binciken NBS Multiple Cluster Indicator Surbey na 2022 kuwa, jihohin Anambra da Enugu sun fara nuna alamomin shiga irin halin da wasu makarantu suke ciki a yankin da ake samun tashin hankali a Arewacin Nijeriya.”
Zargi
Sai dai kuma wasu mazauna yankin da suka zanta da Blueprint Weekend ta wayar tarho sun zargi gwamnatin tarayya musamman Gwamnatin Muhammadu Buhari da nuna halin ko-in-kula kan halin da ake ciki a yankin na Kudu maso Gabas.
Wani mazaunin Enugu Chika Oguchukwu ya ce: “Gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ce za a dora wa alhakin wannan zama a gida. Za mu ci gaba da zama a gida duk ranar Litinin har sai gwamnati ta saki shugabanmu Mazi Nnamdi Kanu.
“Muna fafutukar nemo ‘yancinmu, za kuma mu ci gaba da rufe yankinmu duk ranar Litinin har sai gwamnatin tarayya ta sako mana shugabanmu.
“Wannan doka ta zama-a-gida ta kasance sabuwar al’ada a Kudu maso Gabas. Kamar Kirsimeti da Sabuwar Shekara, ma’aikata suna jin dadin ‘biki’ kuma suna murna. Babban bikin da aka saba yi a yankin a kowace ranar Litinin shi ne, ‘Barka da zaman gida.’ Babu wanda ya damu sosai game da asarar da hakan ke janyowa.
Durkushewar Kasuwanci
Masu kananan sana’o’in da suka zanta da wakilinmu sun koka da yadda zaman ya yi wa sana’o’insu illa, duk da haka, suna tsoron yin magana saboda za a iya kai musu hari, ko ma wasu da ke addabar yankin su kashe su.
Chidibire Asadu, mamallakin katafaren wurin sayar da kayan sawa ne da ke Nsukka, ya ce, “Ba mu ji dadin dokar zama a gida ba, amma abin zai fi shafar ka idan ka fiya korafi sosai. Idan wani daga cikin ma’aikatanka ya sake ya yi magana kan rashin amincewarku da dokar a wajen da ofishinku yake, to ba zato za ku iya ganin mutane da ba a san daga inda suke ba sun mamaye shagonku sun cinna masa wuta.”
Wani karamin dan kasuwa a Jihar Enugu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana lamarin a matsayin abin da ya yi masa illa a harkarsa.
“Asara da muke jawowa abin kunya ne, babu wani kasuwanci da ke gudana a masana’anta saboda gungun marasa kishin kasa suna son hakan kuma gwamnati ta yi shiru.
“Wannan asarar ita ce ke shafar mutum, domin a lokacin da kuka biya ma’aikatanku ladan ayyukan da suka yi muku na kwana 30 bayan kuma suna aiki kasa da kwana hudu ko biyar a sati, to wa ke da asara?”
Har ila yau, wani mai sayar da takalma da ke zaune a Enugu, Uju Ajuonuma, ya ce a halin yanzu dai babu alamar kawo karshen wannan doka.
“Yadda al’amura suke a yau babu wanda ya san karshe wannan lamari, lokacin da ya kamata a ce ‘yan kasuwa sun zama masu hazaka, kirkire-kirkire da samun kudi, a wannan lokaci ne suke gida suna kallon talabijin, akwai matsala fa,” in ji ta.
Misis Grace Onyewuchi, wacce ke sayar da kayan abinci a Kasuwar Relief Enugu, ta ce da wuya kasuwanci ya ci gaba. Ta ce, “A matsayinka na mai sayar da abubuwan da za su iya lalacewa, idan kayanka ba su kare kafin kwanakin zaman gida ba za ka yi asara mai yawa domin za su yi muni kafin ranar kasuwa ta gaba.”
Rikicin kungiyoyin ‘yan kasuwa
A nata ra’ayin, wata kungiyar ‘yan kasuwa ta Ibo mai suna Igbo Business Forum, ta bukaci kungiyar IPOB da ka da ta yi amfani da fafutukar neman kafa kasar Biafra wajen lalata tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas.
Kakakin hukumar, Cif Ndubuisi Ehibundu, ya shaida wa manema labarai cewa a duk ranar Litinin, yankin na asarar biliyoyin Naira saboda dokar zaman gida.
Ya ce: “Ta yaya wasu za su yanke shawarar lalata tattalin arzikin jama’arsu saboda gwagwarmaya? Kuma ku yi tunani, ba su fi mu son Biafra ba. Ta yaya za ku ce wa mutane su zauna a gida alhali ba ku da abin da za ku iya tafiyar da tasirin yunwa a cikin kasa? ‘Yan kasuwa sun yi asarar kusan Naira biliyan 25 a Onitsha kadai. Na yi imanin mu ma mun yi asarar wannan adadi a Aba, Nnewi da sauran wurare, kuma wannan ba zai haifar da da mai ido ba ga tattalin arzikinmu.
“Abokan kasuwancina a wasu shiyyoyin suna jin dadi da irin karuwar da suke samu har ma su yi biki wanda mu kuma shi ne abin da muke asara a nan saboda dokar zaman gida. Me zai faru a yankin Kudu-maso-gabas ne, idan har aka ci gaba da tafiya a haka to hallaka za ta zo wa shiyyar kenan? Wadanda suka saba zuwa Kudu-maso-Gabas don yin kasuwanci sun rabu da mu sun koma Legas maimakon Onitsha, Aba da Nnewi. Muna asara da yawa sakamakon wannan zama a gida.”
Kiraye-kirayen Ohanaeze
Hakazalika, Mataimakin Shugaban Kungiyar Ohanaeze Ndigbo na Kasa, Cif Demian Ogene-Okeke, ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya saki Kanu.
Ogene-Okeke ya ce sakin Kanu, zai kawo karshen da tashe-tashen hankula da ke faruwa a jihohi biyar na yankin, Anambra, Imo, Abia, Enugu da Ebonyi.
Ya roki Shugaba Tinubu da ya kwaikwayi irin afuwar Tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari wanda ya yi wa Cif Chukwumemeka Odumegwu Ojukwu ba tare da wani sharadi ba bayan shafe shekaru 12 yana gudun hijira daga mummunan yakin basasa na watanni 30.
Ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na jin dadin rashin tsaro a kasar Igbo. Da alamu dai gwamnati na goyon bayan cin mutuncin da Asari Dukubo ke yi wa ‘yan kabilar Ibo.
Ogene-Okeke ya ce, “Gwamnatin tarayya na jin dadin kalubalen tsaro da ‘yan asalin yankin da kuma wadanda ba ‘yan asalin yankin Kudu maso Gabas ba ke fama da shi. Kuma da alama gwamnatin ta ji dadin cin mutuncin da Asari Dukubo ke yi.
“Ya kamata su saki shugaban kungiyar ta IPOB kamar yadda kotu ta umarce su, sannan kowane dan Nijeriya zai san ko za a ci gaba da tashe-tashen hankula a yankin ko a’a.”
Wani farfesa a Fannin Tarihi Da Huldar Kasa da Kasa dake Jami’ar Nsukka ta Nijeriya, kuma babban mamba a taron kungiyar ‘yan kabilar Ibo, da ake gudanarwa a shekara-shekara, Damian Osuji, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin Kanu da ke tsare a hannun hukumar DSS.
Osu ya ce sakin Kanu daga hannun jami’an tsaro zai zama matakin farko na samun dawamammen zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas da ke fama da rikici a halin yanzu.
A cewarsa, lauyoyin Nnamdi Kanu na fargabar cewa mafi munin abu zai iya faruwa idan ya ci gaba da zama a hannun DSS; wanda hakan ya ke nuni da fargabar ganin zai iya haifar da barna da kuma kara tabarbarewar tsaro a yankin Kudu maso Gabas.
Ya ce: “Akwai bukatar Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta sakin Kanu domin a yi adalci ga al’ummar Kudu maso Gabas.
Hakan zai dawo da zaman lafiya gaba daya tare da magance tabarbarewar kalubalen tsaro a yankin.
“Ci gaba da tsare Kanu haramun ne saboda akwai umarnin kotun daukaka kara da wata babbar kotu a Umuahia da kuma babbar kotun tarayya da suka ba da umarnin a sake shi.
“Ba za a samu zaman lafiya ba idan Mazi Kanu ya mutu a hannun DSS; haka kuma ba adalci bane ga shugaban na IPOB a bar shi a tsare yana lalacewa.”
Zargin mayar da martani
Ya bayyana fafutukar kafa Kasar Biafra a matsayin “wani abin bakin ciki da yake nuna an mayar da kabilar Igbo saniyar ware.
IPOB ta bayyana a harkokin siyasar Nijeriya ba zato ba tsammani, sai dai kuma ta fara aiwatar da ayyukanta wajen lankaya wa jama’a dokar zaman gida tare da tilasta wa al’ummar yankin Kudu Masu Gabas bin dokar.
Wannan tamkar cinna wa kai wuta ne tun da jama’a da tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas ne za su shiga cikin halin ni-‘ya-su.
“Ina adawa da duk wani mataki da zai cutar da yankin Kudu maso Gabas. Zama a gida ba zai magance matsalar ba; idan muka zauna a gida a Kudu maso Gabas har abada, to ta wacce hanya hakan zai shafi Aso Rock?” in ji Osu.
Ya kuma yi kira ga kungiyar IPOB da ta yi hattara da halin da talakawan Kudancin kasar ke ciki wadanda take ikirarin ba su kariya.
Matakin gwamnati
Amma ga dukkan alamu gwamnatin tarayya ta yunkura wajen ganin ta magance matsalar da ‘yan kungiyar ta IPOB ke haifarwa a yankin, domin a karshen makon da ya gabata, rundunar hadin gwiwa ta sojojin birget na 63 da ke karkashin runduna ta 6, ta sojojin Nijeriya, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na DSS, sun kai hari kan haramtacciyar kungiyar ta IPOB masu ikirarin fafutukar kafa kasar Biara, inda suka lalata wani yanki na ‘yan bindigar Eastern Security Network (ESN) a garin Asaba Jihar Delta, har ma suka yi nasarar cafke daya daga ciki mayakan tare da kwato dinbin makamai.
Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce an kai wannan farmaki ne a ci gaba da gudanar da aikin sharar fage a wasu wurare da aka gano a tsakiyar wani tsauni mai dazuka.
Ya ce sojojin da suka yi artabu da ‘yan ta’addan sun yi galaba a kansu, wanda hakan ya tilasta musu tserewa daga maboyarsu cikin rudani.
Ya kara da cewa sojojin sun kama daya daga cikin mayakan da suka tsere tare da kwato bindigu kirar AK-47 guda biyar, manyan bindigu guda uku, zarto mai amfani da lantarki, bindigar G3 daya da kuma Barrel Gun guda daya.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da harsashi masu rai, adduna, gatari da kuma tutar kungiyar IPOB.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa sojojin ba su tsaya a nan sun ci gaba lalata maboyarsu da ke yankin gami da yin amfani da dabaru a cikin dajin domin fatattakar mayakan da suka tsere.
Ya kara da cewa, Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya yaba wa sojojin da sauran jami’an tsaro bisa kokarinsu na ci gaba da yaki da ‘yan ta’addar, ya kuma bukaci su ci gaba da zage dantse domin dawo da zaman lafiya a yankin.