Dole A Dawo Da Kamfanonin Sayen Amfanin Gona Don Bunkasa Manoma –Sani Brothers

An shawarci gwamnatin Muhammadu Buhari da ta Dawo da kamfanoni masu sayan kayan amfanin Gona kamar yadda akeyi a shekarun baya indai ana kishin bunkasa harkar noma da kuma bunkasa rayuwar manoma a Najeriya.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji sani Yunusa sarina wanda akafisani da Sani Brothers tsohon dan kasuwa kuma masani akan harkar sifiri a kasar nan ya ce a shekarun baya idan kaka tayi Akwai Kamfanoni na Gwamnati da ake kira marketing Board Wanda aikin irin wadannan kamfanoni ko hukumomi na Gwamnati shi ne susaye kayan amfanin Gona da aka noma kamar gyada, Auduga,Wake da makamantansu domin ka da suuyi kwan tai manoma suyi asara.

Haka kuma yakara da cewa su dannan kamfanoni susuke da illimi nasye da siyarwa cikin gida da waje wanda in sunsiya sun san inda zasuje sunemo masu siye da daraja wanda hakan yanasa manoma susamu biyan bukatarsu batareda sun sayar da kayansu ba daraja ba domin rashin irin wanana nasa manoma su siyar ba dfaraja bsakamakon wasu bukakatu dasuke tasowa monoma da kaka na Aurar da ya’ya da sauran bukatu dasuke tilasta masu sai da kayan afarashi da bai dace ba tunda bawani tsari da hukumatayi na kwaucewa koma baya ko asara ga manoma wanda wannan abu yana jawo koma baya ga harkar noma da manoma a Nijeriya.

Haka kuma a matsayinsa na masani aharkar sifiri yace akwai bukatar adawo kan Gaskiya ta hanyar dawo da TOLIJET Akan hanyoyinmu asamu mutane masu Gaskiya ba barayi ba inda za a ruka amfani da kudin domin gyara hanyoyi akan lokaci batare da ambar ramuka akan hanyoyi ba. Haka kuma wajibi ne ayi tsari na kayyade adadin ton na nauyin da kowace mota kattawuce wannan addadi in ta wuce sai aci tarara mai motar hakan zai sa asamu ingancin hanyoyi.

Haka kuma akarshe ya bukaci adawo da ma aikata masu kula da hanyoyi wan da zaka ga gidajensu a bakin hanya duk bayan kilo mita kamar 50 da makamantansu wan aikin su she ne kula da hanyoyi da lafiyar mutane.

 

Exit mobile version