A yayin da ake shirye-shiryen zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 a Kasar Cote d’Iboire, hukumar kwallon kafar Nijeriya NFF, ta fitar da tawagar wucin gadi ta Super Eagles, da ta kunshi kwararrun ‘yan wasa 40 da ke shirin wakiltar kasar.
Mai horar da tawagar Super Eagles Jose Peseiro ya bayyana cewar dole ne a yi taka tsantsan wajen fitar da ‘yan wasan da za su wakilci kasar.
- CNSA: Kasar Sin Na Kiyaye Ra’ayin Bude Kofa Da Kasar Amurka Wajen Yin Mu’amalan Ayyukan Sararin Samaniya
- Yadda Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba Ke Ruruta Ayyukan Ta’addanci
Jadawalin wanda ya kunshi kwararrun matasan ‘yan wasa masu tasowa, an karkasa su mataki-mataki da suka hada da masu tsaron raga shida, masu tsaron baya 13, ’yan wasan tsakiya takwas, da kuma ’yan wasan gaba 13.
Fitattun ‘yan wasan sun hada da mai tsaron raga Francis Uzoho, Adebayo Adeleye, da Stanley Nwabali. Masu tsaron baya; William Troost-Ekong da Kebin Akpoguma wadanda suka yi fice wajen dawo da martabar tsaron tawagar. Akwai jerin gwanon ‘yan wasan tsakiya da suka hada da Aled Iwobi da Wilfred Ndidi, akwai kuma sunaye kamar Bictor Osimhen, Emmanuel Dennis, da Kelechi Iheanacho.
Duk da cewa hukumar NFF ba ta tabbatar da zaben na karshe a hukumance ba, masu sha’awar kwallon kafa sun cika da murna yayin da Super Eagles ke shirin tsallakewa zuwa rukunin A, inda za su fafata da Ekuatorial Guinea, da Cote d’Iboire, da kuma Guinea-Bissau domin neman daukar AFCON.
Tawagar Super Eagles ta ‘yan wasa 40 na wucin gadi a AFCON 2023 kamar haka.
Masu Tsaron Raga 1. Francis Uzoho 2. Adebayo Adeleye 3. Ojo Olorunleke 4. Stanley Nwabali 5. Amas Obasogie 6. Kirista Nwoke Masu tsaron gida; 1. Ola Aina 2. Bright Osayi-Samuel 3. Tyronne Ebuehi 4. Jamilu Collins 5. Zaidu Sanusi 6. Bruno Onyemaechi, 7. William Troost-Ekong 8. Semi Ajayi 9. Calbin Bassey 10. Kenneth Omeruo 11. Kebin Akpoguma 12. Chidozie Awaziem 13. Jordan Torunarigha Yan Wasan Tsakiya; 1. Wilfred Ndidi 2. Frank Onyeka 3. Joe Aribo 4. Aled Iwobi 5. Alhassan Yusuf 6. Fisayo Dele-Bashiru 7. Raphael Onyedika Nwadike 8. Kelechi Nwakali Yan Wasan Gaba 1. Bictor Osimhen 2. Bictor Boniface 3. Terem Moffi 4. Umar Sadik 5. Ahmed Musa 6. Paul Onuachu 7. Cyriel Dessers 8. Ademola Lookman 9. Nathan Tella 10. Musa Saminu 11. Emmanuel Dennis 12. Samuel Chukwueze 13. Kelechi Iheanacho.