Kakakin majalisar wakilan Amurka ta kammala ziyararta a Taiwan ne a jiya Laraba.
Kuma yayin ziyarar, ta nanata wasu batutuwa, kamar na “dokar dangantaka da Taiwan”, tana ikirarin cewa, Amurka ta yi wa Taiwan alkawari, kuma za ta kasance tare da yankin da dai sauransu.
A shekaran jiya, ta wallafa wata kasida a jaridar Washington Post, inda ta dogara da “dokar dangantaka da Taiwan” da “tabbaci shida ga Taiwan”, a matsayin dalilan ziyararta.
Wannan wani rashin kyautawa ce daga bangaren Amurka da kuma keta manufar Sin daya tak a duniya.
Ba shakka, Amurka ce ta yi gaban kanta wajen shirya wadannan dokoki da tabbacin da Pelosi ke ikirari, wadanda suka saba da alkawarin da Amurka ta yi cikin sanarwoyin 3 na hadin gwiwa tsakaninta da Sin. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)