• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Ne Bangaren Amurka Ya Mai Da Martani Ga Duniya Game Da Amfani Da Maganin Kara Kuzari Yayin Wasanni

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Amurka

A halin yanzu, an riga an kammala rabin gasar wasannin Olympics ta Paris ta shekarar 2024, amma a yayin gasar, kafofin watsa labarai da hukumomi na Amurka, suna ta maganganu marasa tushe, tare da yin Allah wadai da ’yan wasan sauran kasashe cewa wai suna shan maganin kara kuzari ba bisa ka’ida ba, amma a sa’i daya kuma, sun kare ’yan wasan kasarsu wadanda aka yiwa gwajin shan maganin kara kuzari a hukumance, wanda hakan ya nuna cewa, Amurka tana da “ka’idoji iri biyu”, ta kuma siyasantar da wasannin motsa jiki, da kuma amfani da su a matsayin makamai.

A ranar 7 ga watan nan, hukumar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta duniya wato WADA, ta ba da sanarwar cewa, tun daga shekarar 2011, a kalla akwai misalai guda uku, inda hukumar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta Amurka wato USADA, ta amince da ’yan wasan da suka yi amfani maganin Steroid da EPO, amma suka samu damar ci gaba da shiga gasa, a maimakon yi musu hukunci.

  • ‘Yan Majalisar Tarayya 29 Da Suka Mutu A Kan Kujerunsu Cikin Shekara 9
  • Martanin ‘Yan Adawa Kan Zanga-zanga Da Jawabin Shugaban Kasa

Sanarwar ta ce, hakan ya sabawa ka’idar WADA, wadda aka tsara don kare mutuncin gasar wasannin motsa jiki, ya kuma gurgunta adalcin gasar wasannin motsa jiki, da kuma yin barazana ga lafiyar ‘yan wasan da abin ya shafa.

A sa’i daya kuma, bisa binciken intanet da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi tsakanin wadanda aka bincika a duk fadin duniya, ya nuna kaso 95.01 cikin dari na wadanda aka bincika da zargin danyen aikin shan maganin kara kuzari a bangaren Amurka, yaki ne da ’yan adawar kasar bisa sunan wasannin motsa jiki, kana kaso 96.84 cikin dari sun yi imanin cewa, bangaren Amurka ya rasa mutunci a idon WADA, kuma kaso 96.11 cikin dari sun yi kira ga sassan kasa da kasa da su bi ruhin Olympics, su kiyaye mutunci, da adalci na hukumomin wasannin motsa jiki na kasa da kasa tare.

Wadannnan ra’ayoyin da shawarwarin sun tabbatar da mummunan aikin da Amurka ta yi a fannin kare amfani da maganin kara kuzari yayin wasannin motsa jiki, kaza lika hakan ya nuna cewa, kasashen duniya na kallon Amurka a matsayin wadda ke kare “babban matsayi” ta ko wane irin hali. (Safiyah Ma)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Masu Bayyana Ra’ayi Sun Zargi USADA Da Yin Rufa-rufa

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Masu Bayyana Ra’ayi Sun Zargi USADA Da Yin Rufa-rufa

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.