• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole ne Japan Ta Dakatar Da Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Da Bin Wata Hanya Mafi Dacewa

by CMG Hausa
2 years ago
Japan

Ran 22 ga wata, gwamnatin Japan ta sanar da cewa, za ta zubar da ruwan dagwalon nukiliyar da take ajiye da shi cikin teku, tun daga gobe Alhamis 24 ga wata. Ta yi biris da rashin jin dadin da jama’ar duniya ke nunawa kan hakan, inda ta sanya jama’ar duniya tunkarar asarar da matakin nata zai haifar.

Jami’ar Tsinghua ta kasar Sin ta yi hasashen cewa, bisa gwajin da ta yi, idan wannan ruwa ya shiga teku, zai isa gabar tekun kasar Sin bayan kwanaki 240, yayin da zai isa gabar tekun arewacin nahiyar Amurka cikin kwanaki 1200. Bayan shekaru 10 kuma, zai shafi dukkanin fadin teku a duniya. Matakin da Japan ke dauka, ba zai nisanta ita kanta da bala’in ba.

  • Shin Japan Biris Za Ta Yi Da Hakkin Al’ummarta Da Na Makwabtaka?

A hakika dai, shirin zai kawowa sha’anin kamun kifi a kasar Japan kalubaloli da dama. Hukuma mai kula da kayayyakin gona, da gandun daji, da teku, ta ba da kididdiga ta shekarar 2022, cewa yawan albarkatun teku da ake samu sun yi kasa tun daga shekarar 1956.

Ban da wannan kuma, kasashe ko yankuna 12, sun yanke shawarar hana shigar da kayayyakin teku daga Fukushima na Japan. Idan gwamnatin Japan ta aikata wannan shiri, to ba shakka kasashen duniya za su kara kayyade shigar da albarkatun teku, da abincin dake da nasaba da hakan daga kasar Japan, lamarin da zai kawo illar ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Al’ummomin kasar Japan, kungiyoyin kasashen duniya, da kasashen dake kewayen tekun Pacific sun yi Allah wadai da batun da kakkausar harshe, inda suka bukaci gwamnatin kasar Japan da ta soke wannan kuduri. Gamayyar kasa da kasa na ganin cewa, batun zubar da ruwan dagwalon nukuliya cikin teku ya saba wa dokar kasa da kasa, kuma zai haddasa matsalolin da ba za a iya warware su ba.

LABARAI MASU NASABA

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Tun lokacin da kasar Japan ta gabatar da wannan shiri yau shekaru 2 da suka gabata, mutanen kasa da kasa suka nuna shakku da damuwa matuka kan ko shirin ya dace da doka ko a’a, ko kuma yana da tsaro ko a’a. Domin sassauta damuwar jama’a, gwamnatin kasar Japan da kamfanin wutar lantarki na Tokyo sun yi alkawari cewa, ba za su zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba, in babu amincewar bangarorin da abin ya shafa kan wannan batu. Amma, mutuncin gwamnatin kasar Japan ya zube sabo da ba ta cika alkawarinta ba.

Ba kawai gwamnatin kasar Japan ta yi karya ga al’ummunta ba, har ma ta yi karya ga gamayyar kasa da kasa cewar, wai shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba zai haifar da matsala ba. A dayan bangare, kasar Japan ta canja ma’anar ruwan dagwalon nukiliya zuwa ruwan tsabtacen nukiliya, domin boye illar da ruwan zai haifar wa al’ummun duk duniya. haka kuma, kasar Japan ta kashe kudade da yawa domin sayan “iznin amincewa” kan shirinta.

Kana, bisa dokar teku ta MDD, kasashen duniya suna da hakkin kiyaye muhallin teku, a matsayin daya daga kasashen da suka sa hannu kan dokar, ya kamata kasar Japan ta dauki alhakinta yadda ya kamata. Kuma, gamayyar kasa da kasa suna da ikon kare kansu bisa doka, da kuma neman diyya daga kasar Japan.

Duniya gidan daukacin bil Adama ne, kuma tsaron teku, da nagartattun muhallinsa, na amfanar jama’a matuka. Shirin da Japan take bi, zai sanya dukkanin fadin duniya yin asara. Ana fatan gwamnatin Japan za ta dakatar da wannan shiri, wanda ba wanda zai ci gajiyarsa, ta kuma nemi wata hanya da ta dace, kada ’yan siyasar kasar sun kare moriyar kansu ta bangarensu kadai, ta sanya duniya cikin mawuyacin hali. (Mai zana MINA Masu Fassara: MINA, Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika
Daga Birnin Sin

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba
Daga Birnin Sin

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
Next Post
Wagner Yevgeny Prigozhin Ya Mutu A Hatsarin Jirgin Saman Rasha

Wagner Yevgeny Prigozhin Ya Mutu A Hatsarin Jirgin Saman Rasha

LABARAI MASU NASABA

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.